Gwamnatin Tarayya Ta Yi wa Sojoji Karin Albashi Mai Gwabi don Inganta Walwalarsu a Najeriya

Gwamnatin Tarayya Ta Yi wa Sojoji Karin Albashi Mai Gwabi don Inganta Walwalarsu a Najeriya

  • Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya ce mafi karancin albashin soja yanzu ya kai N100,000 duk wata
  • Christopher Musa ya ce har yanzu kasafin da ake warewa fannin tsaro ba ha wadatarwa kamar yadda ya kamata
  • Ministan ya kuma musanta rahoton cewa ba a bai wa sojoji ingantacen abinci, yana mai cewa zargin da ake ba gaskiya ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin albashin sojojin Najeriya zuwa N100,000 a wata domin inganta walwalarsu.

Musa ya bayyana cewa an yi wannan kari ne sakamakon sake duba albashin sojoji da gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi a baya-bayan nan.

Ministan tsaro.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Ministan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na News Central, inda ya ce duk da wannan ci gaba, har yanzu bangaren tsaro na fama da karancin kudade.

Kara karanta wannan

Ministan Tsaro: Abin da ya hana sojoji gwabza wa da ƴan bindiga don ceto ɗaliban Oyo

Kasafin tsaro ya yi kadan a Najeriya

Da aka tambaye shi ko kasafin kudin tsaro na yanzu ya isa gudanar da harkokin tsaron Najeriya, Christopher Musa ya amsa da cewa, "Bai wadatar ba."

Sai dai Musa ya ce gwamnatin tarayya ta yi kokari sosai wajen kara albashin jami'an sojoji a irin wannan lokaci da ke fama damatsin rayuwa.

Ya ce:

"Da farko soja yana karbar N49,000 a wata. Mun yi kokari sosai, yanzu yana karbar N100,000."

Ya nemi hukuncin kisa ga masu garkuwa

Ministan ya kuma bukaci a fara zartar da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dakile wannan laifi.

A cewarsa:

"Ina ganin ya kamata a yi hakan. Dole ne a samar da abin da zai tsoratar da masu aikata laifi. Dokokinmu suna da sassauci, shi ya sa mutane ke anfani da hakan.
"Idan sun san duk wanda ya aikata laifi zai fuskanci hukunci mai tsauri, hakan zai zama darasi."

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya kausasa murya kan 'yan bindiga, ya ce a hada kai a yake su

Ya musanta zargi kan abincin sojoji

Christopher Musa ya kuma yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa ana bai wa sojoji abinci mara inganci.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya suna sauraron jawabin kwamanda Hoto: Nigerian Army
Source: Twitter

Ya ce wani soja mai suna Justice Crack ya kirkiri wani yanayi domin ya nuna kamar ba a samar wa sojoji cikakken abinci ba.

A cewarsa:

"Abincin sojojin yana da kyau. Akwai nama da sauran abubuwan da ya kamata su kasance. Amma ya umarci a cire su domin ya nuna kamar ba a ba su ba."

Minista ya ba sojoji izinin harbi

A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaro, Janar Christopher Musa ya ba jami'an tsaro izini su harbe 'yan bindiga da 'yan ta'adda nan take ba tare da jiran wani umarni ba.

Janar Musa ya yi gargadi mai kaushi cewa duk jami'in da ya ki daukar mataki da sunan jiran umarni za a dauke shi tamkar mai hada baki da miyagu.

Musa ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 226 a jihar Sokoto yayin kaddamar da motocin aiki 62 da sauran kayan tsaro da gwamnatin jihar ta saya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262