Sojojin Najeriya Sun Yi Farin Ciki da Karin Albashi, Sun Mika Sabuwar Bukata ga Tinubu
- Wasu dakarun Sojojin Najeriya sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karin albashi da ya yi musu daga kashi 30 zuwa 80
- Hakan na zuwa ne bayan matakin da shugaban kasar ya dauka na yi wa sojoji karin albashi domin inganta walwalarsu
- Sai dai sojojin sun bukaci Tinubu ya sake duba alawus dinsu yayin da ake sa ran ƙarin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wasu sojojin Najeriya sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da karin albashi daga kashi 30 zuwa 80 cikin 100 ga jami'an rundunar sojin kasar.
Sai dai sun bukaci shugaban kasa da shugabannin rundunar soji su sake nazarin alawus da ake ba su domin dacewa da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

Kara karanta wannan
Sunan Minista ya fito a jerin wadanda aka tsara neman tallafinsu don yiwa Tinubu juyin mulki

Source: Facebook
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X, Shugaba Tinubu ya amince da karin albashi ga sojoji kusan 250,000 a ranar Talata.
Sabon tsarin ya tanadi karin albashi da ya kai kashi 80 cikin 100 ga kuratan sojoji zuwa masu mukamin sajan.
Sojoji sake mika bukata ga Tinubu
Wasu daga cikin sojojin da suka zanta da Leadership ba tare da bayyana sunayensu ba sun ce duk da cewa karin albashin abin farin ciki ne, ba zai warware duk matsalolinsu ba.
Wani soja da ke fagen yaki ya ce:
"Ina aiki a yankin da ake gudanar da yaki, na bar katin ATM dina a hannun matata. Bana taɓa albashi na, amma har yanzu bai ishe su ba. Idan ma ina cikin bariki ne, da wannan albashin kadai zan dogara da shi wajen rayuwa."
"Alawus ana bai wa wadanda ke aiki a daji ne kawai. Wadanda ke cikin bariki suna rayuwa ne da albashi kadai. Muna bukatar a sake duba alawus dinmu."
Wani soja kuma ya ce abokan karatunsa sun yi matukar farin ciki da sanarwar karin albashin, kuma suna jiran watan Satumba domin ganin yadda za a aiwatar da shi.
Janar Musa ya yabawa Tinubu
Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya gode wa Shugaba Tinubu bisa amincewa da abin da ya kira karin albashi mai cike da tarihi ga jami'an rundunar sojin Najeriya.
Janar Musa ya ce matakin shugaban kasa ya nuna cewa gwamnatin Tinubu ta ba da muhimmanci ga jin dadin sojojin da ke kare Najeriya.

Source: Twitter
Ya bukaci dakarun rundunar sojin Najeriya su dauki wannan karin albashi a matsayin karin kwarin gwiwa domin su kara jajircewa wajen yaki da ta'addanci, 'yan bindiga, masu satar danyen mai da masu garkuwa da mutane.
Yadda ake biyan sojoji a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya ce mafi karancin albashin soja yanzu ya kai N100,000 duk wata.
Musa ya bayyana cewa an yi wannan kari ne sakamakon sake duba albashin sojoji da gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi.
Ministan ya kuma bukaci a fara zartar da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dakile wannan laifi.
Asali: Legit.ng
