Babbar Magana: Ma'aikata Sun Huro Sabuwar Wuta ga Shugaba Tinubu
- Ma’aikatan Najeriya sun ba Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa ranar 11 ga watan Agusta, 2026, domin ta magance batun wasu hakkokinsu da ba a biya ba
- Majalisar tattaunawa ta ma’aikatan gwamnati ta bukaci a biya bashin karin albashin watannin Maris da Afirilu tare da aiwatar da alawus na musamman na 40%
- Kungiyar ta yi gargadin cewa jinkirin gwamnati na iya haifar da tashin hankali a tsakanin ma’aikata a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja - Ma’aikatan Najeriya sun ba Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa ranar 11 ga watan Agusta, 2026, domin ta magance batun wasu hakkokinsu da ba a biya ba.
Ma’aikatan sun yi gargadin cewa ci gaba da jinkiri na iya haifar da tashin hankali a tsakanin kungiyoyin kwadago a fadin kasar.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ce Majalisar Hadin Gwiwa ta Tattaunawa kan Harkokin Ma’aikatan Gwamnati ta Kasa (JNPSNC) ce ta fitar da gargadin, inda ta zargi gwamnati da kasa daukar mataki kan muhimman batutuwan da suka shafi ma’aikatan gwamnati.

Kara karanta wannan
Badakalar PFIPC: Adeniyi ya yi sabuwar fallasa yayin da yake tsare a hannun 'yan sanda
Daga cikin batutuwan akwai bashin karin albashi da ba a biya ba da kuma aiwatar da alawus na musamman na 40%.
Bukatar ganawa da ministan kudi
A cewar rahoton Vanguard, majalisar ta bukaci a shirya ganawa cikin gaggawa da Ministan Kudi kuma Ministan Kula da Harkokin Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele.
A wata wasika mai kwanan wata 31 ga watan Yuli, 2026, majalisar ta ce ganawar za ta taimaka wajen warware matsalolin da suka dade suna ci gaba da faruwa.
Ma’aikatan sun ce wasikun da suka aika a baya zuwa ofishin ministan ba su samu amsa ba.
An nemi a biya bashin albashi
Daga cikin manyan bukatun ma’aikatan akwai biyan bashin karin albashin watanni biyu na Maris da Afirilu, 2026.
Gwamnatin Tarayya ta bullo da karin albashin ne a shekarar 2023 a matsayin matakin wucin gadi domin rage radadin cire tallafin man fetur da tsadar rayuwa.
Majalisar ta kuma bukaci a aiwatar da alawus na musamman na 40% ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Ta ce an tsara fara biyan alawus din ne daga ranar 1 ga watan Mayu, 2026, bayan Hukumar Albashi, Kudaden Shiga da Albashin Ma’aikata ta Kasa ta fitar da wata sanarwa kan batun.
Ma’aikata sun yi gargadi
JNPSNC ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin jinkirin gwamnati wajen daukar mataki.
Majalisar ta yi gargadin cewa ci gaba da yin shiru kan bukatun na iya kara tayar da hankula a tsakanin ma’aikata.
Ta kara da cewa an sanar da manyan cibiyoyin kungiyoyin kwadago, ciki har da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da Kungiyar Ma’aikata ta Najeriya (TUC), halin da ake ciki.

Source: Facebook
Ko da yake majalisar ba ta bayyana ranar da za a fara yajin aiki ba, ta ce gazawar gwamnati wajen magance batutuwan na iya sa ma’aikata daukar wasu matakai.
Majalisar ta bayyana cewa wa’adin ranar 11 ga watan Agusta na nufin Ministan Kudi ya gana da ita tare da magance bukatunta, ba ranar fara yajin aiki ba.
Wannan sabon ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan tsadar rayuwa da kuma matsin tattalin arziki da ma’aikatan gwamnati ke fuskanta.
Sarki Musulmi ya musanta goyon bayan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tawagar yaɗa labarai ta Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta musanta cewa ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Tawagar ta ce ba zai yiwu Sarkin Musulmi, a matsayinsa na uba ga dukkan 'yan Najeriya, ya fito ya goyi bayan wani ɗan takara ko ya shiga siyasar jam'iyya ba.
Asali: Legit.ng

