Dalilin da Ya Sa Gwamna Abba Ya Kashe N1.5bn don Shirya Auren Gata a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin jihar ta kashe sama da N1.5 biliyan wajen shirin Auren Gata na 2026
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an yi wa dukkan ma’auratan gwaje-gwajen lafiya, shawarwarin aure da horo kafin shigar da su cikin shirin
- Kowace amarya ta samu N100,000 na sadaki da karin N100,000 a matsayin tallafin jari, baya ga kayan daki da abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi karin haske kan dalilin gwamnatinsa na ware N1.5bn domin shirya auren gata.
Gwamna Abba ya ce gwamnatin jihar ta ware sama da N1.5 biliyan wajen shirin Auren Gata na 2026 domin cika alkawarin da ta dauka tare da bai wa ma’aurata 1,500 cikakken tallafin zamantakewa da tattalin arziki.

Source: Facebook
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 8 ga watan Agustan 2026 yayin da yake jawabi a wajen bikin aure da aka shirya wa ma’auratan 1,500 da suka amfana da shirin auren na jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ya ce an kirkiro shirin ne ba wai kawai domin taimaka wa ma’aurata su yi aure ba, har ma da ba su damar fara rayuwar aure cikin samun tallafin zamantakewa, tattalin arziki da na gida.
Alkawarin da aka dauka
Gwamnan ya ce shirin na daga cikin muhimman alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar yayin yakin neman zabe a kananan hukumomin jihar 44 kafin babban zaben 2023.
“Alhamdulillah, dukkan godiya ta tabbata ga Allah, a yau mun ci gaba da cika wannan alkawari,” in ji shi.
A cewarsa, an gudanar da cikakken tantance dukkan ma’auratan da ake sa ran za su amfana kafin shigar da su cikin shirin.
Ya ce tantancewar ta kunshi gwaje-gwajen lafiya, ba da shawarwarin aure, da kuma gudanar da tarukan bita da karawa juna sani domin shirya ma’auratan yadda za su fuskanci nauyin rayuwar aure.
Gwamnan ya ce gwajin lafiya ya kasance muhimmi musamman wajen kare lafiyar ma’auratan da kuma yaran da za su haifa nan gaba.
Tallafin da aka ba ma’aurata
Gwamna Abba ya bayyana cewa kowace amarya ta samu N100,000 a matsayin sadaki, sannan aka ba ta karin N100,000 a matsayin tallafin jari domin ta fara karamar sana’a ta kuma samu dogaro da kanta ta fuskar tattalin arziki.
Haka kuma, ma’auratan sun samu kayan daki da muhimman abubuwan amfani a gida, ciki har da gadaje, katifu da sauran kayan bukatu.
An kuma ba su kayan abinci da wasu tallafi domin rage musu nauyin kudaden da ake kashewa wajen fara sabuwar rayuwar gida.

Source: Facebook
Haruna Bashir ya shiga auren gata
A wani labarin kuma, kun ji cewa Haruna Bashir, mutumin da ya rasa matarsa da 'ya'yansa shida bayan an kashe su a farkon shekarar nan, ya sake yin aure a karkashin shirin auren gata da gwamnatin jihar Kano ta shirya wa ma'aurata 1,500.
An daura auren Bashir ne ranar Juma'a, 7 ga watan Agustan 2026 a Babban Masallacin Juma'a da ke Fadar Mai Martaba Sarkin Kano.
Asali: Legit.ng

