PDP Ta Goyi bayan Gwamnan Kebbi da ke APC domin Tazarce a 2027? Gaskiya Ta Fito
- Jam’iyyar PDP a Kebbi ta yi karin haske game da yada jita-jitar cewa ta nuna goyon bayanta ga gwamnan jihar Kebbi a zaben 2027
- PDP ta yi martanin ne kan rahotannin cewa ta amince da Gwamna Nasir Idris ko tana goyon bayan APC a zaɓen 2027
- Shugaban PDP na Kebbi, Usman Bello Suru, ya ce rahotannin ƙarya ne, yana mai tabbatar da cewa jam’iyyar tana nan ɗaya kuma mai zaman kanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kebbi - An samu wasu rahotanni da ke yawo cewa PDP ta marawa Gwamna Nasir Idris baya domin tazarce a zaben 2027.
Jam’iyyar PDP a Kebbi ta musanta rahotannin cewa ta amince da Gwamna Nasir Idris ko tana goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki.

Source: Twitter
Kebbi: PDP ta musanta goyon bayan APC
Sai dai a wata sanarwa ta musamman, shugaban PDP na Kebbi, Usman Bello Suru, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, cewar Channels TV.
Wannan rade-radin ya biyo bayan amincewar wasu magoya bayan shugaban PDP na ƙasa, Kabiru Turaki, da suka bayyana a ranar Asabar a Birnin Kebbi.
Mutanen sun ce ɓangaren jam’iyyar da ke biyayya ga Turaki ya amince da Gwamna Idris a matsayin ɗan takararsa tilo na zaɓen gwamna na 2027.
Suru ya ce PDP a jihar tana nan cikin haɗin kai da zaman lafiya, kuma ta kasance mai zaman kanta ba tare da goyon bayan APC ba.
Ya ce PDP a Kebbi tana cikin cikakkiyar fahimta da dukkan ’yan takararta da za su fafata a zaɓukan da ke tafe.
“PDP a Kebbi ɗaya ce kuma a haɗe take. Tana cikin cikakkiyar fahimta da dukkan ’yan takararta da za su fafata a zaɓen da ke tafe."
- in ji shugaban.

Source: Original
PDP ta ba magoya bayanta shawara
Suru ya buƙaci ’yan jam’iyya da magoya bayanta su yi watsi da abin da ya kira jita-jitar da ake yaɗawa domin haifar da ruɗani a cikin jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa ya kamata ’yan PDP su mayar da hankali wajen haɗa kan al’umma da ƙarfafa jam’iyyar a shirye-shiryen zaɓukan 2027.
A cewarsa, mutanen da ke yaɗa waɗannan jita-jita ba su da wani iko kan harkokin PDP a Kebbi.
Shugaban ya bayyana cewa jam’iyyar tana da ’yan takarar Majalisar Dokokin Jiha a dukkan ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Haka kuma, PDP tana da ’yan takarar Majalisar Wakilai a dukkan mazabu takwas na tarayya, da ’yan takarar Sanata a dukkan shiyyoyin sanata uku.
Gwamna ya tura bukata ga sojojin Najeriya
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya bukaci rundunar sojin Najeriya ta kawar da ’yan bindiga da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnan ya bayyana hakan yayin ziyarar ba-zata da ya kai sansanin sojoji da ke Yauri, inda ya yaba da jajircewarsu wajen kare al’umma.
Ya ce karin sojojin da aka tura Kebbi zai karfafa yaki da ’yan bindiga, musamman a yankin Yauri, Shanga da Ngaski.
Asali: Legit.ng

