Matsalar Taro: An Rufe Makarantu 65 a Sokoto, Katsina da Wasu Jihohin Arewa
- Akalla makarantun firamare da sakandare 65 ne aka rufe ko suka daina aiki saboda matsalar tsaro a sassan Arewacin Najeriya
- Makarantun da abin ya shafa suna Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi, yayin da rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga karatu a Katsina da Adamawa
- Masana sun yi gargadin cewa ci gaba da rufe makarantu zai ƙara ta'azzara matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta tare da haifar da illoli na dogon lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Akalla makarantun firamare da sakandare 65 ne aka rufe ko suka daina aiki saboda rashin tsaro a sassan Arewacin Najeriya.
Makarantun da abin ya shafa suna cikin jihohin Sokoto, Benue, Plateau, Borno, Kaduna da Kebbi da wasu jihohin Arewacin kasar.

Source: Getty Images
Rufe makarantu a Arewacin Najeriya
Rashin tsaro ya kuma kawo cikas ga harkokin karatu a wasu sassan Katsina, Adamawa da sauran jihohin arewacin kasar, kamar yadda wani bincike da jaridar Sunday Vanguard ta gudanar ya nuna.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda, an kashe fiye da 65 yayin da aka ceto mutane 360
Rufe makarantun ya samo asali ne daga hare-haren ’yan ta’adda da ’yan bindiga, garkuwa da mutane, kauracewar al’umma daga gidajensu da kuma fargabar sake kai hare-hare kan ɗalibai da malamai.
A wasu al’ummomi, an shafe tsawon lokaci makarantu a rufe. A wasu wuraren kuma, hukumomi sun haɗa makarantun da abin ya shafa da wasu makarantu da ke wuraren da suka fi tsaro ko kuma suka mayar da ɗaliban zuwa wasu cibiyoyin karatu.
Wannan yanayi ya sake jawo damuwa kan matsalar yaran Najeriya da ba sa zuwa makaranta, wadda tuni ta yi tsanani, tare da fargabar illar da hakan zai haifar ga makomar ilimin yara.
Matsalar ta ci gaba duk da matakan da gwamnati da ƙungiyoyin bayar da tallafi suka ɗauka tsawon shekaru domin kare makarantu daga hare-hare.
Shirye shiryen gwamnati kan ilimi
Daga cikin matakan akwai Safe Schools Initiative, wadda aka ƙaddamar a shekarar 2014 bayan sace ɗalibai mata 276 daga Government Girls Secondary School da ke Chibok a Jihar Borno.
An kafa shirin ne a matsayin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, Majalisar Ɗinkin Duniya da kamfanoni masu zaman kansu domin kare makarantu da ke wuraren da ke cikin haɗari da kuma tabbatar da cewa yara za su ci gaba da karatu duk da rashin tsaro.
A cewar Global Business Coalition for Education, an tara sama da dala miliyan 30 domin shirin Safe Schools Initiative tun lokacin da aka kafa shi.
Daga baya, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da National Plan on Financing Safe Schools for 2023 to 2026, wanda aka yi hasashen za a kashe Naira biliyan 144.86 wajen aiwatar da shi.
Shirin ya tanadi Naira biliyan 32.58 a shekarar 2023, Naira biliyan 36.98 a 2024, Naira biliyan 37.15 a 2025 da Naira biliyan 38.03 a 2026.
Sai dai sama da shekaru 10 bayan ƙaddamar da Safe Schools Initiative, hare-hare na ci gaba da tilasta wa yara barin makarantu.
Hare-hare na ƙara tsoratarwa
Masana tsaro sun ce hare-haren da ake kai wa makarantu da wasu al’ummomi a jihohi daban-daban na nuna cewa garkuwa da mutane da ’yan bindiga suna sauya salon aikinsu.
Masanin harkokin tsaro, Sam Otoboeze, ya ce matsalar garkuwa da mutane a Najeriya ba ta tsaya kan neman kudin fansa kawai ba, domin ta koma wata hanya ta tsoratar da jama’a da kuma rage amincewarsu da ikon gwamnati na samar da tsaro.
Ya ce yawaitar hare-hare kan makarantu da al’ummomin da ba su da cikakken kariya na nuna cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna zaɓar wuraren da za su iya haifar da babbar fargaba a tsakanin jama’a.
Masana sun gargadi gwamnati
Masana ilimi sun yi gargadin cewa illar rufe makarantu ta fi rashin halartar darussa kawai.
Shugaban Conference of Polytechnics and Colleges of Technology in Nigeria, COREG, Dakta Obini Onuchukwu, ya bayyana yawan rufe makarantu a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar bangaren ilimi.
A cewarsa, dogon lokacin da makarantu ke kasancewa a rufe yana kawo cikas ga jadawalin karatu, tare da sanya makarantu da cibiyoyin ilimi da ke wuraren da rashin tsaro ya shafa samun wahalar cimma sakamakon ilimi irin na takwarorinsu da ke yankunan da suka fi tsaro.

Source: Getty Images
Matsalar yaran da ba sa makaranta
Farfesa Al Chukwuma Okoli, wanda farfesa ne a fannin harkokin tsaro da shugabanci a jami'ar tarayya, Lafia, ya yi gargadin cewa ci gaba da rufe makarantu zai ƙara tsananta matsalar yaran Najeriya da ba sa zuwa makaranta.
Okoli ya ce ana kiyasta cewa akwai yara kimanin miliyan 18.3 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, yana mai gargadin cewa rufe makarantu a al’ummomin da rikici ya shafa na iya ƙara yawan adadin.
Ya ce yaran da suka rasa damar samun ilimin farko na iya fuskantar matsaloli wajen koyon karatu da rubutu da kuma lissafi, lamarin da zai iya sa su kasance cikin haɗarin zama marasa ilimin aiki a rayuwarsu ta gaba.
An rufe makarantu a Edo
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Wani rahoton sirri daga hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ya yi gargaɗin cewa wasu da ake zargi da ta'addanci na shirin sace ɗalibai.
Bayan samun rahoton, gwamnatin jihar Edo ta rufe wasu makarantun sakandare uku da ke ƙaramar hukumar Akoko-Edo domin kariya.
Jami'an DSS sun tabbatar da sahihancin takardar, suna mai jaddada muhimmancin ɗaukar mataki kan bayanan sirri na tsaro.
Asali: Legit.ng


