Ma'aikata Sun Gabatar da Sabon Mafi Karancin Albashin da Suke Bukata a Najeriya

Ma'aikata Sun Gabatar da Sabon Mafi Karancin Albashin da Suke Bukata a Najeriya

  • Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya maida mafi karancin albashi N300,000 a Najeriya
  • Kungiyar Ma'aikatan Tarayya (FWF) ce ta yi wannan kira, tana mai cewa albashin yanzu ba ya daukar dawainiyar ma'aikaci a wata
  • FWF ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta biyan hakkokin da ma'aikata suke bi ciki har da batun mafi karancin albashin N70,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar Ma'aikatan Tarayya (FWF) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan dukkan hakkokin da mambobinta ke bi bashi.

Haka kuma kungiyar FWF ta bukaci gwamnati ta kara mafi karancin albashi zuwa N300,000 tare da daukar matakan gaggawa domin magance matsalolin da suka addabi gidajen gyaran hali a fadin kasar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana ganawa d wasu baƙi a fadr gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa shugaban kungiyar na kasa, Andrew Emelieze, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 6 ga Yuli, 2026 a Abuja.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya aika da sakon ta'aziyya kan rasuwar 'ya'yan tsohon mataimakin gwamna

Ma'aikata sun fara neman hakƙinsu

Ya bukaci gwamnati ta biya tallafin albashi na watanni biyu da ta rikewa ma'aikatan tarayya tun daga watan Yunin 2024, kuma ta biya bashin kaso 40 cikin 100 na alawus na musamman.

Haka zalika, Emelieze ya bukaci gwamnatin Najeriya ta kammala biyan dukkan bashin da ya kamata sakamakon aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Ya ce:

"Muna tunatar da gwamnatin tarayya hakkokin da ma'aikata ke binta, ciki har da karin albashin watanni biyu, bashin alawus na musamman da kuma cikakken aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000."'

FWF ta bukaci a kara mafi karancin albashi

Emelieze ya kuma bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sake duba albashin ma'aikata cikin gaggawa, yana mai cewa albashin da ake biya yanzu ba ya iya biyan bukatun rayuwa saboda tsadar da ake fuskanta.

Ya ce kungiyar na ci gaba da neman a amince da mafi karancin albashi na N300,000, yayin da mafi girman albashi ga ma'aikatan da ke mataki na 17 zai kasance N1.5 miliyan.

Kara karanta wannan

Komai zai fito: APC na shirin fitar da bayanan mataimakin Tinubu a 2027

"Muna sake jaddada bukatar mafi karancin albashi na N300,000 da kuma mafi girman albashi na N1.5m ga ma'aikatan Grade Level 17. Muna jiran matakin gaggawa daga shugaban kasa," in ji shi.
Ma'aikata.
Yadda ma'aikatan gwamnati suka gudanar da zanga-zanga karkashin kungiyar kwadago ta NLC Hoto: NLC HQ Nigeria
Source: Facebook

FWF ta tabo batun jami'an gyaran hali

Baya ga batun jin dadin ma'aikata, Emelieze ya nuna damuwa kan halin da jami'an Hukumar Gyaran Hali ke ciki, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Ya yi zargin cewa jami'ai da dama suna sayen kayan aikinsu da kudinsu, ciki har da kaya, takalma, bel, tambarin mukami da sauran kayan aiki.

Ya kuma yi zargin cewa jami'an da ke rubuta jarabawar karin girma suna tara kudi domin kula da masu gudanar da jarabawar.

Ya ce:

"Muna kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin karbar kudade ba bisa ka'ida ba yayin jarabawar karin girma, tare da inganta jin dadin jami'an gidajen gyaran hali da sauran hukumomin tsaro."

Gwamnatin Tinubu za ta yi karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000.

Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan a wurin taron Good Governance Summit 2026.

Ya ce ce adadin albashin da ake biyan ma'aikata bai dace da halin tattalin arzikin da akebciki ba saboda yadda farashin abubuwa suka kara karuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262