Albashin ma'aikata
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ƙaryata labarin kakaba harajin N40,000 ga ma'aikatan jihar da ake yaɗawa bayan fara biyan mafi ƙarancin albashi.
Gwamnatin tarayya ta fara biyan ma'aikatan jami'o'i albashin da suke bi tare da biyan waɗanda suka yi ritaya hakkinsu, hakan na zuwa bayan NASU ta shiga yajin aiki.
Kungiyar yan kwadago ta TUC ta musanta raɗe-raɗin da ake cewa gwamnatin Benuwai za ta biya N40,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata.
Wani bincike ya bankaɗo matsala a biyan albashin ma'aikatan kasar nan, inda ake fargabar samun jinkirin biyan kuɗin a watanni uku na Oktoba, Nuwamba da Disamba.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamnan ya amince zai biya N72,000 daga watan Nuwamba.
Shugaban NLC, Joe Ajaero a ranar Laraba ya ce su na sane da yadda yan kasa ke kara nutso a cikin talauci saboda yadda tattalin arziki ya sauya a Najeriya.
Sanata Adams Oshiomhole ya bukaci a kara mafi ƙarancin albashi zuwa sama da N70,000. Sanatan ya ce ana kara talaucewa a Najeriya duk da karin albashi da aka yi
Abba Kabir Yusuf ya ayyana N71,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a Kano. A karshen watan Nuwamba za a fara biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi a jihar Kano
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamnan ya amince da zai biya ma'aikata N75,000 a jihar.
Albashin ma'aikata
Samu kari