Da Gaske Yan Bindiga Sun Hallaka Ciyaman da Suka Sace a Zamfara? An Samu Bayani
- An samu wasu rahotanni da ake yadawa a kafofin sadarwa cewa airubutu an kashe shugaban karamar hukumar Bungudu a Zamfara
- Wani bincike ya ce babu wata sahihiyar hujja da ke tabbatar da mutuwar Nura Umar Abdullahi, inda rahotanni suka nuna cewa har yanzu yana nan
- Rahotanni sun tabbatar da cewa babban ɗan’uwan shugaban, Bello Abdullahi, ne ya mutu sakamakon raunukan harbin bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bungudu, Zamfara - Wani rahoto da aka wallafa a kafofin sadarwa ya yi ikirarin cewa an hallak wani shugaban karamar hukuma a Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindiga ne sun kai hari gidan shugaban ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara tare da yin garkuwa da shi da wasu daga cikin iyalansa.

Source: Facebook
Yadda aka yada rahoton kisan ciyaman
Shafi mai suna Hausaland Magazine ya wallafa cewa wasu ’yan ta’adda Fulani sun kashe shugaban karamar hukumar Bungudu ta Zamfara, Nura Abdullahi.
An wallafa wannan ikirari ne a ranar Talata, 4 ga Agusta, 2026, kwanaki bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan shugaban karamar hukumar.
A ranar 25 ga Yuli, 2026, ’yan bindigan sun farmaki gidan Nura Abdullahi a garin Bungudu, inda suka kashe jami’an tsaro huɗu tare da yin garkuwa da shugaban da wasu mutane biyu.

Source: Original
Binciken da aka yi kan rade-radin a Zamfara
Saboda mutane da dama sun ɗauki ikirarin a matsayin gaskiya ba tare da wata hujja ba, Dubawa ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin labarin.
Binciken ya leka kafafen yaɗa labarai masu inganci, amma ba ta samu wata sahihiyar majiya da ta tabbatar da cewa an kashe Nura Abdullahi ba.
Maimakon haka, rahoton Premium Times na ranar 4 ga Agusta, 2026, ya bayyana cewa Bello Abdullahi, babban ɗan’uwan shugaban, ya mutu sakamakon raunukan harbin bindiga da ya samu yayin harin.
Rahoton ya ce ’yan bindiga sun mamaye gidan shugaban a Bungudu ranar 25 ga Yuli, inda suka kashe jami’an tsaro huɗu kafin su yi garkuwa da shugaban da wasu mazauna biyu.
Jaridar Blueprint ma ta wallafa rahoto a ranar 5 ga Agusta, 2026, inda ta tabbatar da cewa babban ɗan’uwan shugaban ne ya mutu, ba shugaban karamar hukumar ba.
Rahotannin biyu sun bayyana cewa Nura Abdullahi yana hannun masu garkuwa da mutane, abin da ya saba wa ikirarin da ke cewa an kashe shi.
Binciken ya kuma tuntubi rundunar ’yan sandan Zamfara domin samun karin bayani, amma kiran wayar kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, bai samu ba.
Haka kuma, binciken ya duba shafin rundunar ’yan sandan Zamfara, amma ba ta samu wata sanarwa da ke tabbatar da mutuwar shugaban ba.
Binciken ya kuma nuna cewa babu wata sanarwa daga gwamnatin Zamfara, rundunar ’yan sanda ko wata hukumar tsaro da ta tabbatar da mutuwar Nura Abdullahi.
Saboda haka, an tabbatar cewa ikirarin cewa an kashe shugaban karamar hukumar Bungudu, Nura Abdullahi, ƙarya ne.
Abin da aka tabbatar shi ne an yi garkuwa da shi ranar 25 ga Yuli, amma babu sahihiyar hujjar mutuwarsa.
Yan sun kusa mamaye sansanonin sojoji
A wani labarin, an ji cewa Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun fatattaki harin 'yan ta'adda kan sansanin soji a Kaura Namoda tare da ceto fararen hula tara da aka sace.

Kara karanta wannan
Wata cuta ta rage mugun iri, ta hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jama'a
Jami'in soja guda da jami'in 'yan sanda guda sun rasu yayin musayar wuta, yayin da sojoji biyu suka jikkata kuma ake ci gaba da ba su kulawa.
Rundunar sojin ta musanta rahotannin da ke cewa jami'an tsaro shida sun mutu, tana mai tabbatar da cewa mutum biyu ne kawai suka rasa rayukansu.
Asali: Legit.ng

