An Mika wa Tinubu Rahoto kan Kara wa Shugaban Ƙasa da Masu Mukaman Siyasa Albashi

An Mika wa Tinubu Rahoto kan Kara wa Shugaban Ƙasa da Masu Mukaman Siyasa Albashi

  • Hukumar RMAFC ta ce ta kammala nazarin albashi da alawus da ake biyan masu rike da mukaman siyasa da na gwamnatin Najeriya
  • Bayan kammala duba batun ne kuma ta ta mika shawarwarinta ga Shugaba Bola Tinubu domin ya yi nazari a kai da kuma amincewa da shi
  • Wannan na zuwa ne a lokacin da kungiyoyin kwadago ke fatan gwamnatin tarayya za ta duba mafi karancin albashin N70,000 da ake biyan ma'aikatan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hukumar Tattara Kudin Shiga, Raba Kasafi da Kula da Albashi (RMAFC) ta bayyana cewa ta kammala aikin sake duba albashi da alawus na masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati.

Ta sanar da cewa bayan ta kammala dogon nazari da aiki a kan batun, an mika shawarwarin da aka cimma ga Shugaban kasa, Bola Tinubu, domin ya yi nazari

Kara karanta wannan

Kiristoci sun samu dama a shirin auren gata da Gwamna Abba zai ƙara yi a Kano

An mika shawarwari game da kara wa masu rike da mukaman siyasa da na gwamnati albashi
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugabar sashen yada labarai da hulda da jama'a ta hukumar, Maryam Yusuf, ta fitar a Abuja.

RMAFC na fifita batun albashi

A ruwayar News Agency of Nigeria, Shugaban RMAFC, Dakta Mohammed Shehu, ya ce hukumar ta kuduri aniyar tabbatar da cewa duk wata bukatar sake duba albashi da alawus na masu mukaman siyasa da na gwamnati tana samun kulawar da ta dace.

Ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin tawagar da mataimakin shugaban majalisar tsofaffin manyan sakatarorin gwamnati na kasa, Elder Akin Arikawe, ya jagoranta.

Mohammed Shehu ya yabawa tsofaffin manyan sakatarorin, yana mai cewa suna daga cikin ginshikan aikin gwamnati saboda gudunmawar da suka bayar wajen tsara manufofi da ci gaban kasa.

Ya ce:

"Babu abin da zai maye gurbin gogewar kwararren ma'aikacin gwamnati. Har yanzu kuna da muhimmiyar rawa wajen tsara manufofi da ba gwamnati shawara kan muhimman batutuwan kasa."

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Katsina ta ce da aka kama shugabannin ƴan ta'adda a filin jirgi

RMFCA ta mika batun karin albashi ga Tinubu

Dakta Mohammed Shehu, kara da cewa hukumar ta riga ta kammala nazarin bukatun da aka gabatar mata tare da tura shawarwarinta ga Shugaba Tinubu.

Ana jiran shugaban kasa ua duba shawarwarin da hukumar RMFCA ta aika masa
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A cewarsa:

"Hukumar ta kammala aikin nazari, kuma muhimman batutuwan da tsofaffin manyan sakatarori suka gabatar sun kasance cikin shawarwarin da aka mika wa Shugaba Bola Tinubu domin ya yi la'akari da su."

Mohammed Shehu ya kuma tabbatar wa tawagar cewa hukumar ta yi nazarin bukatunsu cikin iyakar ikon da kundin tsarin mulki ya ba ta.

Tun da farko, shugaban tawagar, Elder Akin Arikawe, ya ce manufar ziyarar ita ce kara karfafa hadin gwiwa da RMAFC tare da yaba kokarin da take yi wajen magance matsalolin da suka shafi tsofaffin manyan sakatarorin gwamnati.

Gwamnati za ta duba albashin ma'aikata

A wani labarin, mun kawo labarin cewa Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000, wanda a yanzu ake biyan ma'aikatan kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

An ce albashin N70,000 da aka amince da shi a 2024 ya kasance babban ci gaba, amma ya kamata a sake dubawa a yanzu saboda halin rayuwa da kasar nan da jama'a ke ciki saboda matsin tattalin arziki.

Ministan Kwadago Muhammad Dingyadi ya ce ingancin gwamnati yana bayyana ne ta yadda manufofinta ke inganta rayuwar ma’aikata kuma a yanzu akwai bukatar a sake waiwayar mafi karancin albashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng