"Ba Wanda Zai Iya"; Fitaccen Mawaki Davido Ya Cika Baki kan Zaben Najeriya

"Ba Wanda Zai Iya"; Fitaccen Mawaki Davido Ya Cika Baki kan Zaben Najeriya

  • Fitaccen mawakin Afrobeats, Davido, ya ce babu wanda zai iya doke shi a zabe mai inganci da adalci
  • Mawakin ya ce ba shi da shirin shiga siyasa a yanzu saboda rashin gaskiya a tsarin zaben Najeriya
  • Davido ya ce zai ci gaba da mayar da hankali kan harksr waka har sai an samu sahihin tsarin gudanar da zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Abuja - Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ce babu wanda zai iya doke shi a zabe mai inganci da adalci idan ya yanke shawarar neman wani mukamin siyasa a Najeriya.

Sai dai mawakin ya ce ba shi da shirin shiga harkokin siyasa a yanzu, inda ya bayyana rashin gaskiya da yake ganin akwai a tsarin zaben Najeriya a matsayin dalili.

Kara karanta wannan

Sunan Minista ya fito a jerin wadanda aka tsara neman tallafinsu don yiwa Tinubu juyin mulki

Davidd ya ce zai iya lashe zabe a Najeriya
Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido Hoto: Davido
Source: Instagram

Jaridar Vanguard ta ce Davido ya bayyana hakan ne yayin wani tattaunawa kai tsaye da mai kirkirar abubuwan nishadi, Carter Efe, bayan da aka tambaye shi ko zai iya yin takarar gwamnan wata jiha.

Davido ya yi magana kan siyasa

Da yake mayar da martani, mawakin da ya lashe kyaututtuka ya ce zai fi son mayar da hankali kan wakarsa maimakon shiga tsarin zaben da yake ganin ba shi da sahihanci.

“Najeriya da ake rubuta sakamakon zabe? Ba ni da lokacin irin wadannan abubuwa. Domin ni ba irin mutanen da za ka yaudara ba, sannan in je gida in yi barci. Zan dauki mataki idan ka yaudare ni.”

- Davido

Davido ya ce zai yi tunanin neman mukamin siyasa ne kawai idan tsarin zabe ya zama mai gaskiya da bayyana komai a fili.

“Bari na mayar da hankali kan wakata har sai an samu gaskiya da bayyana komai a fili, sannan zan iya shiga takarar mukaman da ake zabe.” In ji shi

Kara karanta wannan

Wike ya sace gwiwoyin Atiku kan daukar Amaechi a matsayin abokin takara a 2027

Davido ya ce zai lashe zabe

Da yake bayyana kwarin gwiwarsa kan yadda ya shahara, Davido ya ce babu wani dan takara da zai iya doke shi idan aka gudanar da sahihin zabe.

“Babu wanda zai iya doke ni a kowane zabe, har abada! A zabe mai inganci da adalci, zan iya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.”

- Davido

Sai dai mawakin ya ce tsarin zaben Najeriya na ci gaba da zama babban cikas ga burinsa na shiga siyasa.

“Akwai matsala da tsarin saboda babu gaskiya da bayyana komai a fili, ana rubuta sakamakon zabe.”

- Davido

Davido ya cika baki kam zabe a Najeriya
Davido fitaccen mawaki a Najeriya Hoto: Davido
Source: Instagram

Davido zai sa ido kan zaben Osun

Davido ya kuma ce zai sa ido sosai kan zaben gwamnan jihar Osun da ke tafe.

“Ina jiran ganin abin da za su yi a zaben gwamnan Osun da ke tafe. Muna kuka.”

- Davido

Ko da yake harkokin siyasa suna da matukar tasiri a cikin dangin Adeleke, Davido ya ce hankalinsa zai ci gaba da kasancewa kan harkar waka har sai an samu karin gaskiya a tsarin zaben Najeriya.

Kara karanta wannan

"Ni masoyinsa ne": Davido ya faɗi yadda ya ke musayar sakonni da Ronaldo

Kudaden da Davido ke kashewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawaki a Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya koka kan tsadar rayuwa.

Fitaccen mawakin wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana cewa yana kashe Naira miliyan 300 zuwa 400, a kowane wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng