'Ya Yi Kadan': Gwamnatin Tinubu Za Ta Sake Duba Mafi Ƙarancin Albashin N70, 000

'Ya Yi Kadan': Gwamnatin Tinubu Za Ta Sake Duba Mafi Ƙarancin Albashin N70, 000

  • Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin sake duba mafi ƙarancin albashi na N70,000
  • An ce albashin N70,000 da aka amince da shi a 2024 ya kasance babban ci gaba, amma ya kamata a sake dubawa
  • Ministan Kwadago Muhammad Dingyadi ya ce ingancin gwamnati yana bayyana ne ta yadda manufofinta ke inganta rayuwar ma’aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta nuna alamun cewa tana shirin sake duba mafi ƙarancin albashi na ƙasa na N70,000.

Gwamnatin ta ce adadin bai ƙara dacewa da halin tattalin arzikin da ake ciki ba saboda yadda farashin abubuwa suka kara karuwa.

Gwamnatin Tinubu za ta sake suba mafi ƙarancin albashi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan yayin taron Good Governance Summit 2026, cewar Vanguard.

Yadda Tinubu ya kara mafi karancin albashi

Kara karanta wannan

'Kashi 80 na matsalolin tsaro da suka addabi Sakkwato na da alaka da miyagun kwayoyi'

Rahotanni sun ce wannan mataki na zuwa ne ƙasa da shekara biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi.

An kara albashin ne daga N30,000 zuwa N70,000 tare da rage lokacin sake dubawa daga shekara biyar zuwa uku.

Ya ce gwamnatin na fahimtar cewa tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, kuma ma’aikata sun cancanci albashin da zai iya tafiya daidai da sauye-sauyen tattalin arziki.

A cewarsa:

“A watan Yulin 2024, Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar mafi ƙarancin albashi na N70,000, fiye da ninki biyu na N30,000 da ma’aikata suka dade suna karɓa.”

Ya ƙara da cewa gwamnati ta rage lokacin sake duba albashi daga shekara biyar zuwa uku domin albashi ya kasance yana tafiya daidai da gaskiyar halin tattalin arziki.

Za a sake duba mafi ƙarancin albashin N70,000
Shugaba Bola Tinubu da Femi Gbajabiamila. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Gwamnati za ta duba kan mafi ƙarancin albashi

Gbajabiamila ya ce albashin N70,000 wanda ya kasance babban ci gaba a shekarar 2024 ya kamata a sake tantance shi cikin gaskiya bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu.

Haka kuma ya bukaci ƙungiyoyin ƙwadago su ci gaba da tattaunawa da gwamnati, yana mai cewa haɗin kai da fahimtar juna sun fi rikici wajen samar da mafita ga ma’aikata da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sakkwato ta yi magana kan rahoton da ake yadawa game da Bello Turji

Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Dingyadi, ya ce tasirin manufofin gwamnati a rayuwar ma’aikata shi ne ainihin ma’aunin kyakkyawan shugabanci, cewar Tribune.

A cewarsa, manufofi ba su kamata su tsaya a rubuce cikin takardu kawai ba, dole ne su samar da ingantacciyar rayuwa, aiki mai kyau, ƙarin ƙwarewa.

Ya ce:

“Ainihin ma’aunin shugabanci shi ne yadda manufofi ke haifar da ingantacciyar rayuwa, aiki nagari, ƙarin samar da kayayyaki, kariyar zamantakewa da mutunci ga ma’aikata.”

Ma'aikata sun nemi karin albashi

Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun nuna cewa ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun buƙaci a ƙara masu albashi da kashi 400 cikin 100 a kan N70,000 na yanzu.

Ma'aikatan sun bayyana cewa tsadar rayuwa ta jefa da yawa daga cikin su a mawuyacin hali, ta inda N70,000 ba za ta iya tsinana masu komai ba.

A cikin jerin bukatun da ta gabatar, kungiyar ma'aikata ta nemi gwamnati ta farfaɗo da tattalin arziki, ƙarfafa darajar Naira da inganta makamashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.