Ba Saban ba: Shugaban APC Ya Cire Adawa, Ya Yaba wa Ƴan PDP kan Ƙoƙarinsu

Ba Saban ba: Shugaban APC Ya Cire Adawa, Ya Yaba wa Ƴan PDP kan Ƙoƙarinsu

  • Shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba wa kungiyar PDP “Rainbow” da sauran jam’iyyu kan goyon bayan Bola Tinubu a 2027
  • Yilwatda ya ce yana da yakinin Tinubu zai bai wa INEC damar gudanar da zabe mai inganci, gaskiya da adalci a 2027
  • Shugaban APC ya bukaci ’yan Najeriya su hada kai, tare da goyon bayan kokarin gwamnatin tarayya na ciyar da kasar zuwa babban matsayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba wa wasu mambobin kungiyar PDP a Najeriya.

Nentawe ya yaba wa “Rainbow” da sauran jam’iyyun siyasa kan bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban APC ya yabawa ƙungiyar PDP kan Tinubu
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda. Hoto: Professor Nentawe Yilwatda.
Source: Twitter

Wannan yabo ya zo ne kwanaki kadan bayan dan takarar gwamnan Taraba kuma mamba a kungiyar, Emmanuel Bwacha, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu a zaben 2027, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Saƙon da Bola Tinubu ya tura wa 'yan ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya da wasu ƙasashe

Ƙungiyar PDP karkashin Wike ta bi Tinubu

Majiyoyi amintattu sun tabbatar da cewa kungiyar tana da alaka da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Farfesa Yilwatda ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai tallafa wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) wajen gudanar da zabe mai ’yanci, adalci da gaskiya a babban zaben 2027.

Shugaban APC ya ce Shugaba Tinubu, kasancewarsa dan dimokuradiyya, ba zai tsoma baki cikin harkokin zabe domin fifita wani mutum ko wata jam’iyyar siyasa ba.

Ya kawo nasarar jam’iyyar adawa a kan APC a zaben gwamnan Anambra da sauran zabuka a matsayin shaida cewa gwamnatin Tinubu ba ta tsoma baki domin tabbatar da nasarar APC ba, cewar TVC News.

Farfesa Yilwatda ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi aiki domin tabbatar da hadin kan kasa, tare da bai wa gwamnatin tarayya goyon baya wajen kokarin ciyar da Najeriya zuwa mataki mafi girma.

Kara karanta wannan

PDP ta goyi bayan gwamnan Kebbi da ke APC domin tazarce a 2027? Gaskiya ta fito

Kungiyar PDP karkashin ta goyi bayan Tinubu
Ministan Abuja a Najeriya, Nyesom Wike. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Twitter

Shawarar Nentawe ga ƴan adawa a Najeriya

Har ila yau, a baya shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ba da muhimmiyar shawara ga ƴan adawa yayin da ake shirin yin zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.

Nentawe ya bukaci 'yan adawa su daina sukar gwamnati kawai Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce ya kamata 'yan siyasa su gabatar da ingantattun hanyoyin magance kalubalen tattalin arzikin Najeriya.

Yilwatda ya ce cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin ceto tattalin arzikin kasar daga durkushewar kasafin kudi.

Shugaban jam'iyyar na kasa ya bayyana tsarin tallafin da ake yi a baya a matsayin wanda ba zai dore ba, yana mai cewa ya amfanar da wasu tsirarun masu gata ne kawai, yayin da ya hana kasar kudaden da take bukata domin muhimman ayyukan ci gaba.

APC ta dora sunayen ƴan takararta

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta kammala loda sunayen dukkan ‘yan takararta na gwamnoni, mataimakan gwamnoni da majalisun jihohi a shafin INEC.

Kara karanta wannan

Daga sama har ƙasa: Gwamna ya mallakarwa Tinubu ƙuri'un jiharsa a 2027

Jam’iyyar ta ce ta loda sunayen ‘yan takarar gwamnoni da mataimakan gwamnoni 56 da na majalisun jihohi 1,015.

Shugaban APC, Nentawe Yilwatda, ya ce nasarar ta nuna karfin tsari da shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.