N70000 Ta Yi Kadan: NLC Za Ta Sake Zama da Tinubu kan Sabon Mafi Karancin Albashi

N70000 Ta Yi Kadan: NLC Za Ta Sake Zama da Tinubu kan Sabon Mafi Karancin Albashi

  • Kungiyoyin NLC da TUC sun ce za su fara tattaunawa da gwamnatin Bola Tinubu kan sabon mafi karancin albashi daga watan Yulin 2026
  • Kungiyoyin sun bayyana cewa a yanzu albashin N70,000 ya rasa tasiri saboda hauhawar farashi da tsadar rayuwa da ake fama da ita
  • 'Yan kwadago dai sun yi watsi da duk wani yunkuri na kakaba haraji kan mafi karancin albashi, tare da gargadi kan talauta masu karamin karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kungiyoyin kwadago na Najeriya, wato NLC da TUC, sun bayyana aniyarsu ta sake bude tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata.

Kungiyoyin sun ce ma’aikata ba za su iya ci gaba da jure wa tsadar rayuwa da hauhawar farashi ba, wanda ke ci gaba da rage darajar kudaden shigarsu.

Kara karanta wannan

'Zabe ne a gabansa': Yan majalisa sun dura kan Tinubu game da tsaron ƙasa

NLC, TUC za su fara zama da gwamnatin tarayya kan mafi karancin albashi.
Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC na Najeriya na magana a ranar ma'aikata. Hoto: @NLCHeadquarters
Source: Facebook

NLC, TUC sun nemi karin albashi

Sun bayyana matsayinsu ne a wata sanarwar hadin gwiwa da suka gabatar yayin taron kungiyar kwadago ta duniya karo na 114 da aka gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland, in ji rahoton Punch.

Kungiyoyin sun ce suna neman abin da suka kira "albashin da zai iya biyan bukatun rayuwa", maimakon tsarin albashin da ake amfani da shi a yanzu.

A cewarsu, karin farashin abinci, sufuri, gidaje da kula da lafiya ya sa mafi karancin albashin da ake biya a yanzu ya daina dacewa da halin da ma’aikata ke ciki.

Sun kuma yi fatali da duk wani shiri na sanya haraji kan mafi karancin albashi ko kara wa masu karamin karfi wasu nauyin kudade.

Yaushe za a fara nazarin sabon albashi?

A ranar 18 ga Yulin 2024 ne aka sanya hannu kan dokar sabon mafi karancin albashi na N70,000 bayan yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ware rukunin 'yan bindigan da zai yi sulhu da su idan ya zama shugaban kasa a 2027

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da amincewa da sabon albashin a ranar 19 ga Yulin 2024, sannan ya fara aiki daga ranar 29 ga watan.

Da farko an tsara a rika duba albashin duk bayan shekaru uku, amma Gwamnatin tarayya ta sanar a watan Janairun 2025 cewa za a rika yin bitar albashin duk bayan shekaru biyu.

Wannan ya sa shekarar 2026 ta zama lokacin da za a sake nazarin tsarin albashin.

NLC ta ce za ta tattauna da gwamnatin Tinubu domin a kara albashin da zai wadaci Najeriya.
Wakilan kungiyoyin kwadago, NLC, TUC a lokacin ganawa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: @NLCHeadquarters
Source: Twitter

NLC da TUC sun yi gargadi kan haraji

Shugabannin kwadagon sun bayyana cewa da zarar sun dawo Najeriya za su sake rubuta wa gwamnati domin neman a fara tattaunawar kafin wa’adin watan Yulin 2026.

Voice of Nigeria ta ruwaito 'yan kwadagon suna cewa:

"Dokar albashin da ake da ita yanzu za ta kare nan gaba kadan, saboda haka za mu bukaci gwamnati ta fara tattaunawa domin kauce wa jinkirin da aka saba samu a baya."

Kungiyoyin sun kara da cewa hauhawar farashi, faduwar darajar naira da tsadar kayayyaki sun jefa ma’aikata cikin mawuyacin hali.

A cewarsu, kakaba haraji kan mafi karancin albashi zai kara talauta jama'a tare da kara tsananta matsin tattalin arziki da ake fama da shi.

Kara karanta wannan

Jika ta kashe kakarta bayan lakada mata duka, an kashe mai shekara 96 da tabarya a Katsina

Lokacin tattauna sabon albashi a Najeriya

Tun da fari, mun ruwaito cewa, NLC, TUC sun bayyana cewa za su fara shirin sake tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin daga watan Yulin 2026, domin kauce wa duk wani jinkiri.

Shugabannin ƙungiyar NLC da TUC ne suka bayyana hakan a bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2026 da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da ake gab da fara tattaunawar albashi, kungiyar kwadago ta yi gargadin cewa rashin hadin kai zai karya karfin hadin gwiwar ma’aikata a kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com