Wata Sabuwa: Gwamna Ya Rage Albashin Ma'aikata Suna Sa Ran Za a Kara Masu
- Gwamnatin jihar Taraba ta tabbatar da ta rage albashin masu share tituna daga N15,000 zuwa N10,000 duk da korafi da ake kan tsadar rayuwa
- Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta danganta lamarin da daukar wasu sababbin ma’aikata da karancin kudin shiga da take da shi
- Bayan rage kudin, an bayyana cewa shugaban hukumar tsaftace muhalli a jihar ya ce wadanda ba su gamsu da tsarin albashin ba za su iya barin aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Taraba - Rahoto ya nuna cewa gwamnatin jihar Taraba ta rage albashin ma’aikata da share tituna daga N15,000 zuwa N10,000.
Ta bayyana cewa hakan ya zama dole domin samar da gurbi ga sababbin ma’aikatan da aka dauka aiki a hedkwatar jihar da kananan hukumomi.

Source: Facebook
An rage albashi a jihar Taraba
Tribune ta wallafa cewa Shugaban hukumar kula da muhalli ta jihar Taraba, Hon. Illiya Kefas, ya tabbatar da rage albashin yayin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo.
A cewarsa, an dauki matakin ne bisa umarnin Gwamna Agbu Kefas domin sarrafa albarkatun da ake da su, sakamakon daukar sababbin ma’aikata.
“Eh, ba mu biya masu share tituna N15,000 ba a wannan watan; mun biya kowannensu N10,000,”
In ji Hon. Kefas.
An fara daukar masu-share titunan ne a shekarar 2023, inda gwamnatin jihar ta rika ba su alawus na wata-wata na N20,000.
Sai dai a watan Maris na shekarar 2024, an ce an bukace su su amince da rage musu N5,000 ko kuma su rasa ayyukansu, wanda hakan ya rage abin da suke samu a wata zuwa N15,000.
Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan sun karbi N10,000 a watan Mayun 2026, wanda ya nuna karin ragi daga adadin da aka cimma yarjejeniya a baya.
Dalilin rage albashin ma'aikatan a Taraba
Da yake karin bayani kan matakin, Kefas ya ce jihar na kokarin daidaita nauyin kudin da ke kanta bayan daukar dimbin sababbin ma’aikata aiki.
Daily Post ta wallafa cewa karancin kudin da jihar ke samu daga asusun tarayya ma ya taimaka wajen daukar matakin rage albashin.
A wani sakon tes da ya aika wa manema labarai, shugaban hukumar ya kare matakin rage albashin, yana mai cewa ma’aikatan da ba su gamsu da tsarin ba suna da damar barin aikin
“Ina da ikon neman mutanena su yi aiki kan N10,000. Duk wanda yake so zai yi aikin, wanda kuma ba ya so zai iya tafiya,”
In ji shi.
Hakan na zuwa ne lokacin da aka ji 'yan kwadago suka bayyana cewa za a sake zama domin ganin an yi wa ma'aikata karin albashi a Najeriya.
Ma'aikatan sun fara koka wa cewa bada N70, 000 a matsayin mafi karancin albashi ya yi kadan.

Source: Getty Images
An nemi karin albashi a Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnonin Najeriya sun nuna cewa akwai bukatar kara mafi karancin albashi a kasar nan.
Gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq ne ya bayyana haka a wani taro da suka yi.
Shugaban gwamnonin ya ce akwai bukatar a dawo da mafi karancin albashi zuwa N100,000 lura da matsalolin tattalin arziki da ake fama da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


