Gwamnatin Osun Ta Sanya Wani Abu a Aljihun Ma'aikata ana Shirin Zaben Gwamna

Gwamnatin Osun Ta Sanya Wani Abu a Aljihun Ma'aikata ana Shirin Zaben Gwamna

  • Gwamnatin jihar Osun karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta sake bai wa ma’aikatan gwamnati tallafin rage radadin matsin tattalin arziki
  • Mai magana da yawun Gwamna Ademola Adeleke ya ce an biya tallafin ne domin kara wa ma’aikata albashi da rage masu radadi
  • Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin kokarinta na inganta walwalar ma’aikata da kara musu kwarin gwiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Osogbo, Osun - Gwamnatin jihar Osun karkashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta sake biyan ma’aikatan gwamnati a fadin jihar tallafin rage radadin matsin tattalin arziki.

Gwamnatin ta ce an dauki matakin ne a wani bangare na kokarinta na inganta walwalar ma’aikata da kuma taimaka musu wajen fuskantar kalubalen tattalin arziki.

Gwamna Adeleke ya ba ma'aikata tallafi
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun Hoto: Pelumi Olajengbesi
Source: Facebook

Mai magana da yawun Gwamna Ademola Adeleke, Olawale Rasheed, ya sanar da biyan tallafin a wata sanarwa da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na X ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya samu sako mai zafi bayan rufe asusun gwamnatin Osun

Ya ce wannan mataki ya nuna yadda gwamnatin Adeleke ta himmatu wajen tallafa wa ma’aikatan gwamnati.

“A wani bangare na jajircewarmu wajen kula da ma’aikatan jihar Osun, wadanda su ne ginshikin gwamnatinmu, mun sake biyan tallafin rage radadi domin kara musu albashi.”

- Olawale Rasheed

Gwamnati ta fadi dalilin bayar da tallafin

Rasheed ya ce gwamnatin Adeleke ta fara biyan ma’aikata tallafin lokaci zuwa lokaci tun kafin aiwatar da sabon karin mafi karancin albashi.

Ya bayyana cewa matakin ya nuna yadda gwamnatin ta ba walwalar ma’aikata muhimmanci.

“Abin lura shi ne mun fara biyan tallafin rage radadi lokaci zuwa lokaci tun kafin aiwatar da sabon karin mafi karancin albashi, wanda ya sanya Osun cikin jihohin farko da suka dauki irin wannan mataki a Najeriya.”

- Olawale Rasheed

An kwatanta gwamnatoci

Gwamnatin jihar ta kuma kwatanta yadda take kula da walwalar ma’aikata da tsarin gwamnatin da ta gabata.

A cewar sanarwar:

Kara karanta wannan

EFCC ta rufe asusun gwamnatin jiha sukutum, an jefa gwamna a matsala dab da zabe

“Wannan ya sha bamban da gwamnatin da ta gabata, wadda ta mayar da talauci wata hanya ta gallaza wa jama’a tare da hana ma’aikatan gwamnati albashinsu da hakkokinsu da suka cancanta.”
"Gwamnatinmu ta himmatu wajen tabbatar da cewa ana mutunta wadanda ke yi wa jihar hidima, kuma ana ba su hakkokinsu da ya dace.”
Adeleke ya gwangwaje ma'aikatan Osun
Gwamna Ademola Adeleke na jawabi a wajen taro Hoto: Pelumi Olajengbesi
Source: Facebook

Gwamnatin ta ce ci gaba da biyan tallafin na daga cikin babban tsarinta na mayar da kwarin gwiwa ga ma’aikatan gwamnati.

Ta kara da cewa shirin zai taimaka wajen inganta kwazon ma’aikata, jawo kwararrun ma’aikata da kuma kara ingancin ayyukan da ake bai wa al’ummar jihar Osun.

Gwamnan Osun ya kalubalanci shugaban EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kalubalanci shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Ola Olukoyede.

Gwamna Adeleke ya kalubalanci Olukoyede ya bayyana dalilin da ya sa aka bayar da umarnin rufe asusun gwamnatin jihar Osun.

Adeleke ya bayyana rufe asusun a matsayin abin da ya saba wa doka, yana mai cewa hakan na mayar da dimokuradiyyar Najeriya abin dariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng