An Rage Mugun Iri da 'Yan Sanda Suka Kashe Hatsabibin Jagoran 'Yan Bindiga
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasarar kashe wani da ake zargi da jagorantar ‘yan ta’adda a Imo
- Ojiogu Elumah Martin, wanda aka fi sani da “Acid”, ya mutu ne bayan musayar wuta da jami’an STS-FID
- ‘Yan sanda sun kwato bindigar AK-47 da harsasai 56 a maboyar da ake zargin ‘yan kungiyar ke amfani da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza Daudawa ƙwararren edita ne a fannin labarai, siyasa da al'amuran yau da kullum, wanda ke da gogewa wajen nazarin al'amuran da suka shafi Najeriya
Owerri, jihar Imo – Jami’an Rundunar Musamman ta ‘Yan Sandan Najeriya (STS-FID) sun kashe Ojiogu Elumah Martin, wanda aka fi sani da “Acid”, wanda ake zargi da jagorantar wata kungiyar masu aikata laifuka a karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo.
“Acid”, wanda ake zargin yana da hannu wajen kisan wani basaraken gargajiya na jihar Imo, Eze Paulinus Ekwueme, da wasu mutum biyar a kan titin Asa/Awara, ya samu munanan raunuka yayin wata musayar wuta da jami’an tsaro a maboyarsa da sanyin safiyar 6 ga watan Agusta.

Source: Twitter
Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, CSP Ani Iniedu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a karshen mako, cewar rahoton The Nation.
Jami’ai sun kai samame maboyar
A cewar Iniedu, jami’an sun isa maboyar wanda ake zargin ne da misalin karfe 1:30 na dare, inda ya bude musu wuta bayan ya gan su.
Hakan ya haifar da musayar wuta da ta dauki tsawon sa’o’i, kafin jami’an su raunata wanda ake zargin har ya mutu.
An gudanar da aikin ne karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, ACP Victor Ogbeide Godfrey, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) Olatunji Rilwan Disu, a wani bangare na kokarin cafke wadanda ake zargi da hannu wajen kisan basaraken.
An kwato AK-47 da harsasai
‘Yan sanda sun ce sun kwato bindigar AK-47 guda daya, magazina uku da harsasai 56 masu rai kirar 7.62mm daga wurin, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Sai dai an ce wasu mambobin kungiyar sun tsere zuwa cikin daji yayin samamen.
Binciken farko ya nuna cewa “Acid” shi ne ake zargin jagoran wata kungiyar masu aikata laifuka da ke da alaka da jerin kashe-kashe a Ohaji/Egbema da garuruwan da ke makwabtaka da yankin tsakanin shekarar 2024 zuwa 2026.
An danganta shi da kisan basarake
Daga cikin abubuwan da ‘yan sanda ke bincike a kai akwai kisan basaraken Ochia, Eze Ekwueme, da wasu mutum biyar a ranar 10 ga Afrilu 2026 a kan titin Asa/Awara.
Rahotanni sun ce basaraken ya dawo Najeriya ne bayan shafe kusan shekaru biyar a Amurka, kuma an kai masa harin ne a lokacin da yake tafiya Owerri bayan ya halarci wani taro a Ochia, masarautarsa.

Source: Original
Sauran wadanda aka kashe tare da shi sun hada da Amadi Uchechukwu Emmanuel, Onyivara Maduabuchi Jornadad, Gift Broaddic, Abraham Lincoln da Otor Benjamin.
‘Yan sanda sun kuma danganta kungiyar da kisan Emeka Ebere Nwaele a ranar 12 ga Mayu, wanda ake zargin “Acid” ya shirya bayan ya yi zargin cewa Nwaele ne ya bayar da bayanan da suka kai ga cafke wani dan kungiyar mai suna Chinwendo Mirabe, wanda aka fi sani da “K2”.
An kashe yaron hatsabibin dan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen jagoran 'yan bindiga Ado Aleiro ya fuskanci babban koma-baya yayin artabu a jihar Katsina.
Majiyoyi sun bayyana cewa dan bindigar ya rasa ɗansa, wasu ’yan uwa takwas da babura kusan 30 a Katsina.
Asali: Legit.ng


