Sakon da Bola Tinubu Ya Tura Wa 'Yan Dariƙar Tijjaniyya a Najeriya da Wasu Kasashe

Sakon da Bola Tinubu Ya Tura Wa 'Yan Dariƙar Tijjaniyya a Najeriya da Wasu Kasashe

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura wakili wurin maulidin Sheikh Ahmad Al-Tijani, RTA, wanda ya gudana a jihar Kano
  • A jawabin da ya tura, Tinubu ya bukaci shugabannin Tijjaniyya da mabiyansu na duniya su kauce tare da yakar tsattsauran ra'ayi
  • Shugaban kasar ya ce bai kamata a yi amfani da addini wajen halatta kashe-kashen fararen hula ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabannin addini da su rika yin kakkausar magana kan ta’addanci, garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga.

Tinubu ya yi wannan kira ne ranar Lahadi a Kano, cikin sakon da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya isar a madadinsa yayin babban taron Mauludin Sheikh Ahmad Al-Tijani, RTA.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a taron Majalisar dinkin duniya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sakon da ya isar ga yan Tijjaniyya a Kano

Kara karanta wannan

Sakon Abba ga Malamai, Sarakuna da Gwamnonin da suka halarci auren gata a Kano

Vanguard ta ruwaito cewa Tinubu ya tura wannan sako ne ga Khalifan Darikar Tijjaniyya na duniya, malamai, shugabannin addini da mabiya daga Najeriya da sauran kasashe.

Shugaba Tinubu ya ce malaman addini na da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile tashin hankali, tsattsauran ra’ayi da amfani da akida wajen tayar da rikici.

“Dole ne a rika jin muryoyinku a kai a kai kan kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da amfani da addini wajen halatta zalunci,” in ji Tinubu.

Ya kuma bukaci kungiyoyin addini da hanyoyin sadarwarsu su kara karfafa wayar da kan jama’a kan zaman lafiya, ilimin addini, karatu da kuma tarbiyyar matasa masu nagarta.

"Ba a bautar Allah da kashe mutane"

Tinubu ya jaddada cewa ba za a iya cewa ana bautar Allah ta hanyar lalata rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Ya ce:

“Sama da komai, iyayenmu malamai su ci gaba da koyar da cewa babu wata ibada ta gaskiya ga Allah da za ta ci gaba ta hanyar lalata rayuwar mutumin da Allah ya sanya ta zama mai tsarki.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya aika saƙo cikin kaɗuwa da aka tabbatar da rasuwar babban malami a Najeriya

Ya kuma bayyana cewa taron na gudana ne a lokacin da duniya ke fuskantar rikice-rikice, rashin tabbas, sauyin yanayi, matsalar abinci da makamashi, ta’addanci da laifukan da suka ketare iyakokin kasashe.

Maulidi.
Khalifan Tijjaniyya na duniya da wasu malamai a wurin maulidin Sheikh Ahmad Tijani RTA a Kano Hoto: Ahmad Sani
Source: Facebook

Tinubu ya yaba wa Tijjaniyya

Shugaban ya ce Darikar Tijjaniyya, wadda ke da dimbin mabiya a Yammacin Afirka, Arewacin Afirka da sauran sassan duniya, na da muhimmiyar damar taimakawa wajen sasanta rikice-rikice da yaki da tsattsauran ra’ayi,

Ya ce gwamnati ta aminta da muhimmiyar rawar da malaman addini da sarakuna ke takawa wajen karfafa zaman lafiya a tsakanin al’umma, dakile yada labaran karya da kuma inganta zaman tare.

Shugabannin Tijjaniyya sun ziyarci Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Koli ta Tijjaniyya ta duniya ta kai wa Shugaba Bola Tinubu ziyarar ta'aziyya kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.

Tawagar daga Aljeriya, Najeriya da Senegal ta wakilci sama da mambobi miliyan 400 na darikar a duniya wajen mika sakon ta'aziyya ga Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262