Ma'aikata Za Su Warwasa, Shugaba Tinubu Ya Shirya Cika Alkawarin da Ya Dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara biyan ragowar tallafin albashi da ta yi wa ma'aikata alkawari kafin tsakiyar watan Agusta
- Ministan Kudi, Taiwo Oyedele ya ce gwamnatin tarayya tana cika alkawuran da ta dauka ga ma'aikata domin inganta walwalarsu
- Kungiyar JPSNC ta bukaci gwamnati ta gaggauta warware sauran matsalolin da ma'aikata ke fuskanta a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ma'aikatan gwamnati cewa za ta fara biyan ragowar tallafin albashi (wage award) kafin tsakiyar watan Agusta, 2026.
Ministan Kudi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele nr ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin kungiyar Joint Public Service Negotiating Council (JPSNC) karkashin jagorancin Kwamared Kabiru Ado Minjibir.

Source: Twitter
Daily Trust ta ce sanarwar da Ma'aikatar Kudi ta fitar ta ce ministan ya bayyana cewa gwamnati ta fara magance wasu daga cikin matsalolin da kungiyar ta gabatar tun kafin ta karbi takardarta a hukumance.
Tinubu zai cika alkawarin tallafin albashi
A cewar ministan, ana kammala dukkan matakan da suka dace domin amincewa da biyan ragowar tallafin albashin, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa ma'aikatan da suka cancanta za su fara karbar kudaden kafin tsakiyar watan Agusta.
Ya ce:
"Idan gwamnati ta dauki alkawari, tana cika shi. Ba dabi'armu ba ce mu yi alkawarin da ba za mu iya cikawa ba. Idan akwai sauran batutuwa, za mu bayar da sahihin jadawalin lokaci sannan mu tabbatar da aiwatar da su."
Oyedele ya kuma bayyana cewa gwamnatin na bai wa batun karin girma muhimmanci, inda ake ci gaba da sarrafa sauran jerin sunayen ma'aikatan da suka rage bisa tsarin da aka amince da shi.
Ya umarci jami'an da abin ya shafa da su gaggauta duba takardun da kungiyar JPSNC ta gabatar tare da hada kai da ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati domin hanzarta warware duk wasu matsalolin da suka shafi ma'aikata.
Ministan ya amince cewa kungiyoyin kwadago sun nuna damuwa kan jinkirin aiwatar da wasu yarjejeniyoyi, amma ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da gina amincewa ta hanyar gaskiya, tattaunawa da kuma daukar matakan gaggawa.

Source: Twitter
Bukatun da ma'aikata suka mika
Tun da farko, shugaban kungiyar JPSNC ya bukaci gwamnati ta hanzarta warware matsalolin da suka hada da ragowar tallafin albashi, bashin karin girma, matsalar daidaiton albashi ga ma'aikatan lafiya da sauran batutuwan jin dadin ma'aikata.
Ya ce aiwatar da wadannan alkawura cikin lokaci zai kara tabbatar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da ma'aikata tare da kara musu kwarin gwiwa.
Ma'sikata sun yi watsi da tayin N100,000
A wani labarin, kun ji cewa ana ci gaba da sukar tayin gwamnonin Najeriya na kara mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnati daga N70,000 zuwa N100,000.
Kungiyar ma'aikatan gwamnatin tarayya (FWF) ta yi watsi da tayin gwamnonin, tana mai cewa adadin bai dace da halin da ma'aikata ke ciki ba.
Asali: Legit.ng

