Maganar N500,000 Ake Yi, Sabuwar Bukatar NLC ga Gwamnati kan Albashin Ma’aikata
- Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara mafi karancin albashin ma’aikata saboda tsananin matsin tattalin arziki
- Mataimakin shugaban NLC na kasa, Audu Titus Amba, ya ce wa’adin karin albashin N70,000 da aka cimma yarjejeniya ya kare tun watan Yuli
- Gwamna Nasir Idris ya ce zai gabatar da bukatar kungiyoyin kwadago a taron Gwamnonin Najeriya, bayan ya fara biyan ma’aikatansa N75,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabannin Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC, da Kungiyar TUC sun bukaci sake fasalin mafi karancin albashin ma'aikata
Kungiyoyin sun bukaci gwamnatin tarayya ta amince da N500,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatan Najeriya.

Source: Facebook
Mataimakin Shugaban NLC na Kasa kuma Shugaban Kungiyar Malaman Najeriya, NUT, Kwamared Audu Titus Amba, ne ya bayyana hakan a taron da aka yi a Birnin Kebbi, cewar Leadership.
Wa'adin karin N70,000 ya cika
Amba, wanda ya wakilci Shugaban NLC na Kasa, Kwamared Joe Ajaero, ya ce wa’adin karin N70,000 da aka cimma tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya ya kare a watan Yuli.
Ya ce saboda haka kungiyoyin kwadagon na son sake komawa teburin tattaunawa da gwamnatin tarayya domin neman a biya ma’aikatan kasar sabon mafi karancin albashi na N500,000.
Amba ya ce a halin da ake ciki, duk wani mafi karancin albashi da bai kai N500,000 ba ba zai iya biyan bukatun ma’aikata ba, saboda tsananin matsin tattalin arziki da suke fuskanta.
Shugaban NLC ya bayyana cewa kungiyoyin kwadagon ba sa neman fada da gwamnatin tarayya, sai dai suna son sake tattaunawa domin duba mafi karancin albashin ma’aikata bisa la’akari da halin da suke ciki.
Amba ya yaba wa Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, saboda samar da yanayin da ya dace domin gudanar da taron, wanda ya samu halartar wakilai kusan 1,000.

Source: Facebook
Kokarin da Gwamna Nasir Idris ya yi
Da yake bude taron, Gwamna Nasir Idris ya tunatar da kungiyoyin kwadago cewa shi ne gwamna na farko da ya aiwatar da biyan mafi karancin albashi na N75,000 ga ma’aikatansa.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin gabatar da sabuwar bukatar kungiyoyin kwadagon a daya daga cikin tarukan Kungiyar Gwamnonin Najeriya, cewar Punch.
Kungiyoyin kwadagon sun ce bukatar karin mafi karancin albashi na zuwa ne saboda yadda tsadar rayuwa da matsalolin tattalin arziki suka kara yin tsanani ga ma’aikatan gwamnati.
Sun bayyana cewa sabon tsarin albashin da za a tattauna zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da ma’aikata ke fuskanta.
NLC da TUC sun kuma jaddada cewa suna son cimma matsaya da gwamnatin tarayya ta hanyar tattaunawa, ba ta hanyar rikici ko adawa ba.
Bukatar N500,000 na zuwa ne bayan da aka fara aiwatar da mafi karancin albashin N70,000 da gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago suka cimma yarjejeniya a baya.

Kara karanta wannan
Farfesa Rabi'a daga Kano ta yi magana kan mukamin da aka naɗa ta a Majalisar dinkin duniya
Ana fafatukar neman karin albashi
An ji cewa rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun buƙaci a ƙara masu albashi da kashi 400 cikin 100 a kan N70,000 na yanzu.
Ma'aikatan sun bayyana cewa tsadar rayuwa ta jefa da yawa daga cikin su a mawuyacin hali, ta inda N70,000 ba za ta iya tsinana masu komai ba.
A cikin jerin bukatun da ta gabatar, kungiyar ma'aikata ta nemi gwamnati ta farfaɗo da tattalin arziki, ƙarfafa darajar Naira da inganta makamashi.
Asali: Legit.ng

