Gwamnatin Kano Ta Garzaya Kotu bayan Kuskuren Tura sama da N5m Wani Asusu
- Hukumar Fansho ta Jihar Kano ta bayyana yadda aka samu kuskuren hannu aka aika kudin fanshon wani bawan Allah ga wani daban
- Ta yi bayani cewa kuskuren ya samo asali ne daga wurin rubuta lambobin ƙarshe na asusun wanda ya sa kuɗin suka shiga wani asusu daban
- Hukumar ta fara daukan matakai da za su taimaka wajen tilasta wa bankin dawo da kudin domin a dauki matakin tura wa wanda ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar Fansho ta Jihar Kano ta garzaya gaban kotu domin karɓo kuɗaɗen fansho da yawansu ya kai N5,346,587.16.
Wannan shari'a ta samo asali ne saboda kuskure da aka yi waen tura kudin tsohon ma'aikacin ga wani asusu na daban a maimakon wanda ya dace a ba shi hakkinsa.

Source: Facebook
Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa daraktan Kuɗi na hukumar, Sunusi Aminu Rano, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli, 2026.
Hukumar fanshon Kano ta yi kuskure
Sunusi Aminu Rano, ya kara da cewa kuskuren ya faru ne yayin tattara bayanan masu karɓar fansho kafin a biya su ta bankin Jaiz Bank.
A cewarsa, an yi kuskuren rubuta lambobi biyu na ƙarshe na asusun wanda ya kamata a tura kuɗin zuwa. Maimakon a rubuta "83", sai aka rubuta "38", lamarin da ya sa kuɗin suka shiga wani asusu daban.
Sanarwar ta ce wannan kuskuren rubutu ne ya haddasa tura kuɗin ga wanda ba shi ne ya kamata ya karɓa ba kuma har aka fara neman a dawo da su.
Hukumar fansho ta tafi kotu
Rano ya bayyana cewa da zarar hukumar ta gano abin da ya faru, nan take ta tuntubi Jaiz Bank tare da sanar da bankin cewa an yi kuskuren tura kuɗin.
Sai dai bankin ya bayyana wa hukumar cewa bisa ƙa'idojinsa da dokokin da ke tafiyar da harkokin banki, dole ne a samu umarnin kotu kafin a iya janye ko mayar da kuɗin daga asusun da suka shiga.

Source: Original
Saboda haka, Hukumar Fansho ta ce ta riga ta fara matakan shari'a domin samun wannan umarnin, wanda ake sa ran zai fito ranar Litinin 20 ga watan Yuli, 2026.
Da zarar kotun ta bayar da umarnin, za a miƙa shi ga Jaiz Bank domin bankin ya mayar da kuɗin cikin gaggawa zuwa inda ya dace.
Hukumar ta nuna takaicinta kan abin da ya faru, tana mai tabbatar wa masu karɓar fansho da al'ummar jihar cewa za ta warware matsalar cikin gaskiya tare da bin dukkan matakan doka.
Gwamnatin Kano ta yi kuskure
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta yi kuskure yayin da take kokarin tura kudin giratuti na wani ma’aikaci, inda aka aika N5.3m zuwa asusun wani mutum da ke zaune a jihar Neja maimakon wanda ya kamata ya karba.
Rahotanni sun nuna cewa mutumin da kudin suka shiga asusunsa bai yi yunkurin anfani da su ba. Maimakon haka, ya fara kokarin ganin an mayar da kudin ga gwamnati, amma hakan bai yi nasara ba.
Bayan haka, mutumin ya tuntubi dan jarida Ja’afar Ja’afar domin ya taimaka wajen isar da sakon cewa kudin ba nasa ba ne, yana mai bukatar a dauke su daga asusunsa a mayar wa gwamnatin Kano ko kuma wanda ya cancanci karbar su.
Asali: Legit.ng

