Amurka
Rahotanni daga Iran sun nuna cewa kasar ta ki yarda ta koma zagaye na biyu na tattaunawa da Amurka saboda wasu sharudda masu tsauri da matakan Trump.
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya yabawa dakarun sojojin kasar. Ya yaba da kwazonsu wajen kare kasar daga yakin da aka dora maya.
Rundunar sojojin Iran ta IRGC ta sanar da tarwatsa wasu masu yi wa Isra'ila, Amurka da Birtaniya leken asiri. Ta ce mutanen na shirin tayar da tarzoma a kasar.
Kasar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa ba gudu ba ja da baya, a shirye take ta kare kanta daga duk wanda ya kai mara hari, amma ta ve ba ta kaunar a yi yaki.
Rundunar sojin Iran ta IRGC ta sanar da toshe mashiga Hormuz bayan zargin Donald Trump da karya sharadin sulhu da suka kulla kafin bude shi ranar Juma'a.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa za su iya cigaba da kai hare-haren bama-bamai a Iran idan ba a cimma wata yarjejeniya ba da Tehran.
A labarin nan, za a ji cewa an fara hangen jiragen dakon mai sun fara wuce wa ta mashigar Hormuz da Iran ta rufe bayan Amurka da Isra'ila sun kai mata hari.
Shugaban majalisar dokokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya fito ya karyata ikirarin da Donald Trump ya yi kan mashigar Hormuz.
Gwamnatin Musulunci ta Iran ta musanta kalaman shugaban Amurka Donald Trump,ta ce babu kasar da za ta yarda ta kwashe gaba daya sinadarin Uranium dinta.
Amurka
Samu kari