Ana cikin Musayar Yawu tsakanin Iran da Amurka, Mojtaba Khamenei Ya Fitar da Sabon Sako
- Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya aika sako ya taya murnar zagayowar ranar kafa rundunar sojojin kasar
- Mojtaba Khamenei ya taya dakarun kasar murnar zagayowar ranar inda ya yaba masu kan yadda suke kare kasar
- Sabon jagoran addinin ya kuma karrama manyan kwamandojin Iran da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kaddamar kan kasar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Sabon jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Seyyed Mojtaba Khamenei, ya jinjina wa dakarun ƙasar.
Mojtaba Khamenei ya jinjina wa dakarun ne saboda jarumtakar da suka nuna wajen kare ƙasar a yaƙin da aka tilasta musu kwanan nan, kamar yadda suka yi a yaƙoƙin baya.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta ce Mojtaba Khamenei ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya fitar domin murnar 29 ga Farvardin, ranar da aka kafa rundunar soojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a hukumance.

Kara karanta wannan
Ana shirin sake zama, Trump ya fadi abin da zai harzuka Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Mojtaba ya yabawa sojojin Iran
Ya bayyana cewa rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana nan tana "kare ƙasa, ruwa, da tutar da take ƙarƙashinta cikin jarumtaka" a yayin fuskantar yaƙin cin zarafi da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar.
"Tare da babban tallafi na Allah da na al'umma, da kuma dakarun da ke haɗe kafada da kafada da sauran mayakan sauran rassan tsaro, rundunar ta fuskanci dakarun sojoji guda biyu waɗanda ke sahun gaba na kafirci da girman kai, inda ta bayyana rauninsu da kaskancinsu a idon duniya."
- Mojtaba Khamenei
Barazana ga makiyan Iran
Mojtaba Khamenei ya jaddada cewa kamar yadda jiragen yaki marasa matuƙa na Iran suke kai hare-hare kamar walkiya a kan Amurka Isra'ila, haka rundunar sojan ruwa take a shirye domin ɗanɗana wa makiya kudarsu.
Saƙon, wanda aka fitar a ranar da marigayi wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, Imam Khomeini, ya ware domin girmama sojoji, ya taya daukacin jami'an sojoji, iyalansu, da al'ummar Iran murna.
Ayatollah Mojtaba Khamenei ya bayyana nasarar juyin juya halin Musulunci a matsayin babban sauyi a tarihin rundunar sojojin kasar, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.

Source: Getty Images
Mojtaba Khamenei ya karrama shahidai
Jagoran ya kuma karrama daukacin kwamandojin da suka jagoranci rundunar sojojin Iran a cikin shekaru 50 da suka gabata, waɗanda da dama daga cikinsu sun yi shahada.
Daga cikin waɗanda ya ambata har da fitattun kwamandoji irinsu Qarani, Fallahi, Namjou, Fakouri, Babaei, Setari, Ardestani, Sayyad Shirazi, da kuma shahidan baya-bayan nan, Seyyed Abdolrahim Mousavi da Aziz Nasirzadeh, waɗanda duka biyun suka yi shahada a yaƙin kwanaki 40 da aka tilasta wa ƙasar.
Iran ta yi wa Trump martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna damuwa kan yawan surutun da Donald Trump, yake yi kan yakin da ake yi.
Hakan na zuwa ne bayan yawan samun maganganu masu cin karo da juna daga Shugaba Trump, musamman bayan fara tattaunawar sulhu tsakanin kasasshen Amurka da Iran.
Gwamnatin Iran ta caccaki Shugaba Trump kan yawan magana, tana mi cewa ya cika surutu mara amfani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
