Soke Kudin Tsaro da Wasu Sauye Sauye da ADC za Ta Kawo idan Ta Ci Zaɓen 2028

Soke Kudin Tsaro da Wasu Sauye Sauye da ADC za Ta Kawo idan Ta Ci Zaɓen 2028

  • Jam'iyyar hadakar adawa ta ADC ta fara bayyana kadan daga cikin manufofinta idan yan Najeriya suka amince da zabarta a 2027
  • Daga cikin abubuwan da ta jero akwai ce za ta soke kudin tsaro da aka aikawa shugabanni daga kananan hukumomi zuwa tarayya kai tsaye
  • Haka kuma jam’iyyar ta tabo batun almubazzarancin kudin tafiye-tafiyen jami’an gwamnati tare da amfani da kadarorin gwamnati wajen biyan bukatar kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta yi garambawul mai yawa kan yadda ake kashe kudaden gwamnati idan ta samu nasara a zaben shekarar 2027.

Jam’iyyar ta ce daga cikin matakan da za ta dauka akwai soke tsarin kudin tsaro na musamman da tsaurara dokokin tafiye-tafiyen jami’an gwamnati.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Jerin jami'o'i 20 da ASUU ta fara shirin dakatar da harkokin karatu a Najeriya

ADC ta fara fito da manufofinta a kan Najeriya
Yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa a ADC tare da manyan jam'iyya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ADC ta ce matukar aka zabe ta, za ta hana amfani da motocin gwamnati, gidaje, jiragen sama da sauran kadarorin wajen harkokin kashin kai.

Alkawarin ADC ga yan Najeriya

A ruwayar Daily Post, ADC ta bayyana hakan ne a cikin kundin manufofinta na shafuka 25 mai suna ‘The Orange Book’, wanda Sakataren Yada Labaran jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya gabatar a Abuja ranar Talata.

Jam’iyyar ta ce manufar sauyin shi nerage almubazzaranci, karfafa rikon amana da kuma hana karkatar da kudaden gwamnati zuwa abubuwan da za su inganta rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa.

ADC ta tabo tsaro a kundin tsare-tsarenta game da Najeriya
Atiku Abubakar yayin jawabi a wurin karbar tutar takarar jam'iyya a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

A cewar ADC, duk wani kudin da gwamnati za ta ware domin tsaro zai kasance karkashin kulawa, amincewa da binciken majalisa bisa dokokin kasa.

Jam’iyyar ta ce hakan zai taimaka wajen rufe hanyoyin karkatar da kudaden jama’a ko amfani da su ba bisa ka’ida ba kamar yadda ta yi zargin ana yi yanzu.

Kara karanta wannan

Jami'ar ABU ta waiwayi Farfesa Abdullahi, wanda aka ce yana da PhD 5, MSc 5 da digiri 7

ADC na shirin rage almubazzaranci

ADC ta ce za ta takaita tafiye-tafiyen cikin gida da na kasashen waje da jami’an gwamnati ke yi zuwa wadanda suka zama dole, suka shafi aiki kai tsaye kuma suke da amfani ga gwamnati.

Ta ce ba za ta amince da manyan tawagogin tafiye-tafiye ba, sannan ba za a bar jami’ai su tafi da ‘yan uwa ko abokan siyasa a matsayin bangaren tawaga ba.

Da take magana kan yaki da cin hanci, ADC ta ce:

"Za a dauki duk wani batunn karkatar da kudin jama'a a matsayin ta'addanci."

'Dan takarar ADC ya yi barazana

A wani labarin, kun ji cewa Ibrahim Alamin Little da ke takarar gwamnan jihar Kano a inuwar jam'iyyar ADC, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sha kaye a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Ɗan takarar na ADC ya kuma bayyana Abdulkadir Shehu Bari a matsayin abokin takararsa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara duk da cewa har yanzu akwai batu da ke kasa yana dabo game da takarar.

Ibrahim Alamin Little ya yi alƙawarin mayar da hankali kan ilimi, lafiya da bunƙasa matasa idan ya samu damar zama gwamna tare da bayyana yakinin cewa zai yi nasara idan lokacin zabaen ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng