Gwamnatin Tinubu Ta Kafa Tarihi, Ta Kawo Sababbin Dokoki game da Talla a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla a Abuja, domin ƙarfafa tsari, sa ido da ƙwarewa a masana'antar talla
- Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya buƙaci kotun ta gudanar da ayyukanta cikin gaskiya, 'yanci da adalci
- Shugabar kotun, Cecilia Olatoregun, ta yi alƙawarin tabbatar da gaskiya, yayin da ARCON ta bayyana kotun a matsayin ta farko a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sababbin tsare-tsare game da yadda ake gudanar da talla.
An ƙaddamar da sabuwar Kotun Laifukan Talla, a wani mataki na ƙarfafa tsari da sa ido kan harkar talla, inganta ƙwarewa.

Source: Facebook
An kaddamar da kotun talla a Najeriya
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a wurin ƙaddamar da kotun a Abuja kamar yadda ma'aikatar ta wallafa a Facebook.
Idris ya ce manufar gwamnatin ita ce gina masana’antar talla da za ta kasance abin koyi wajen ƙirƙire-ƙirƙire, samun amincewar jama’a da kuma tabbatar da ɗaukar nauyi.
Ya ce:
“Mu gina masana'antar talla da za ta yi fice wajen ƙirƙire-ƙirƙire, ta samu amincewar jama'a kuma ta kiyaye ɗaukar nauyi."
A cewarsa, dokar ta tanadi kafa kotun da za ta saurari laifukan da suka shafi dokar, ƙa’idoji da dokokin da ke kula da lamarin talla.
Idris ya buƙaci kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Cecilia M. A. Olatoregun ta tabbatar an yi ayyukanta cikin gaskiya, ’yanci da adalci.
Ya ce duk wata shari’a da aka gabatar a gaban kotun ya kamata a yi hukunci a kanta bisa hujjojin da ke gabanta, ba tare da tsoro, son rai, ƙauna ko ƙiyayya ba.
A cewarsa:
“Duk wata shari'a da aka gabatar, ku duba ta bisa hujjoji, ba tare da tsoro ko nuna son kai ba, ko ƙauna ko ƙiyayya ko nuna son kai ba."

Source: Facebook
Alkawarin da ministan yada labarai ya yi
Ministan ya tabbatar musu cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da tallafa wa ARCON wajen gina masana’antar talla.
Darakta-Janar na ARCON, Dakta Olalekan Olumuyiwa Fadolapo, ya bayyana kafa Kotun Laifukan Talla a matsayin wani babban ci gaba wajen ƙarfafa bin dokoki da ƙa’idoji.
Fadolapo ya ce kotun ta kasance wata babbar dama ga masana’antar talla ta Nijeriya, yana mai cewa kafa irin wannan kotu wata hanya ce ta hangen nesa wajen inganta tsarin gudanar da harkar talla.
Shugabar Kotun Laifukan Talla, Mai Shari’a Cecilia M. A. Olatoregun, ta yi alƙawarin cewa kotun za ta gudanar da ayyukanta cikin gaskiya, adalci da ƙwarewa.
Tinubu ya fadi yadda ake yi da bashi
Kun ji cewa Fadar Shugaban Kasa ta kare manufar karɓo bashi ta Bola Tinubu ke yi, wanda ya fara jawo maganganu daga yan adawa da masu sharhi.
Hadimin Shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ana ganin inda kuɗin ke tafiya ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa.
Bayo Onanuga ya lissafo wasu ayyuka da ya kira manya-manya, wanda ya ce kadan ne daga cikin hanyoyin da Tinubu ke kashe basussukan da ya amso.
Asali: Legit.ng

