Tinubu Ya Yayyafa Ruwan Sanyi bayan Kalaman Jingir Sun Ta da Kura

Tinubu Ya Yayyafa Ruwan Sanyi bayan Kalaman Jingir Sun Ta da Kura

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kiristoci na da matukar muhimmanci wajen ci gaban Najeriya baki daya
  • Tinubu ya bayyana haka ne a yayin da gwamnatin tarayya da Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za su gudanar da taron tsaro na ƙasa da ƙasa a Abuja
  • Haka kuma kalaman sun zo a gabar da ake cece-kuce game da kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir wanda daya ne daga cikin magoya bayansa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira da a ƙara ƙarfafa tattaunawa da fahimtar juna tsakanin Musulmi, Kiristoci da mabiya sauran addinai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana matsayar shugaban a ranar Litinin 10 ga watan Agusta, 2026 yayin ƙaddamar da sabon masallacin Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya a Abuja.

Kara karanta wannan

NLC ta bude kofar tattaunawa da gwamnati, ma'aikata na iya samun karin albashi

Shugaba Tinubu ya yi magana kan hadin kan addinai a Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Muhammad Idris ya ce Najeriya da Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za su gudanar da wani taron tsaro na ƙasa da ƙasa a Abuja ranar Talata11 ga watan Agusta, 2026 domin tattauna hanyoyin inganta zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da tsaro.

Za a yi taro a Abuja - Gwamnatin Tinubu

The Nation ta ruwaito cewa Ministan ya ce taron ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke ƙoƙarin ƙara inganta tsarin tsaron ƙasa tare da aiwatar da sauye-sauye da zuba jari domin bunƙasa tattalin arziki da ci gaban ƙasa.

Ya ce shugaban Bola Tinubu ya kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya da sauran sassan duniya.

Najeriya za ta hada babban taro ka matsalar tsaro
Mohammed Idris, Ministan yada labarai da wayar da kai Hoto: Ministry of Information and National Orientation
Source: Facebook

A kalamansa:

“Shugaban ya kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba kawai a Najeriya ba, har ma a faɗin duniya. Wannan wata alama ce ta hanyar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke bi."

Kara karanta wannan

Tinubu zai hallara a taron Izala da kungiyar Musulmin duniya za su yi

Ya ƙara da cewa kasancewar Najeriya ƙasa mafi yawan al'umma a Afrika ya sa take da alhakin taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar.

Gwamnati: 'Najeriya na da muhimmanci'

A cewarsa, samar da kasa Najeriya cikin zaman lafiya da tsaro zai taimaka wajen inganta zaman lafiya a yammacin Afrika da kuma sauran sassan nahiyar.

Mohammed Idris ya ce taron zai ba shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki damar musayar ra'ayoyi da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya, tsaro da fahimtar juna.

Ya kuma yaba wa Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya, Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), gwamnatin Saudiyya da sauran waɗanda suka taimaka wajen kawo Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa Najeriya.

Kwankwaso ya tsawatar kan rikici a Najeriya

A wani labarin kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya shiga cikin jerin wadanda suka soki kalaman Sheikh Sani Yahaya Jingir kan tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027.

Tsohon gwamnan Kano wanda shi ne dan takarar mataimakin shugaban Kasa a NDC ya ce irin waɗannan kalamai na iya raba kan al’umma tare da jefa gaba a tsakanin mazauna kasar nan.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce mutanen Kano ba sa goyon bayan kalaman Jingir, yana mai kira ga shugabannin siyasa da addini da su ƙarfafa haɗin kai a maimakon tunzura mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng