Yawan Surutun Shugaban Amurka, Trump Ya Jawo Masa Martani Mai Zafi daga Kasar Iran

Yawan Surutun Shugaban Amurka, Trump Ya Jawo Masa Martani Mai Zafi daga Kasar Iran

  • Yawan maganganun da Shugaban Amurka, Donald Trump ke fitowa yana yi sun fara jan hankalin gwamnatin kasar Musulunci ta Iran
  • Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh ya nuna damuwa kan kalaman Trump, yana mai cewa ya cika surutu barkatai
  • Ya kuma nanata matsayar Iran cewa ba ta kaunar yaki, amma a shirye take ta kare kanta ko da kuwa za a kashe sojojinta gaba daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Kasar Musulunci ta Iran ta fara nuna damuwa kan yawan surutu barkatai da Shugaban Amurka, Donald Trump ke fitowa yana yi kan rikicin Gabas ta Tsakiya.

Ana yawan samun sabani da maganganu masu cin karo da juna daga Shugaba Trump, musamman bayan fara tattaunawar sulhu tsakanin kasasshen Amurka da Iran.

Shugaba Trump da Khamenei.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Donald J. Trump, Anadou Ajensi
Source: Getty Images

Kasar Iran ta soki Shugaba Donald Trump

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa gwamnatin Iran ta caccaki Shugaba Trump kan yawan magana, tana mi cewa ya cika surutu mara amfani.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ne ya fito ya soki kalaman Shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan kamar batun sinadrin uranium da mashigar ruw at hormuz.

Ya bayyana cewa shugaban na kasar Amurka na “yawan magana” tare da furta maganganu masu rikitarwa.

Khatibzadeh ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a gefen taron diflomasiyya na Antalya da aka gudanar a ƙasar Turkiyya.

Iran ta kira Trump da mai yawan surutu

Da aka tambaye shi kan kalaman Trump na baya-bayan nan, inda ya yi barazanar cewa Amurka za ta “ci gaba da jefa bama-bamai” idan ba a cimma yarjejeniya da Iran ba zuwa ranar Laraba, jami’in na Iran ya ce kalaman sun ci karo da juna.

Trump dai ya yi ikirarin cewa Amurka za ta iya ci gaba da kai hare-hare Iran, amma awanni kadan kafin furta wadannan kalamai, an ji shi yana cewa saura kiris su cimma yarjejeniyar sulhu.

Kara karanta wannan

Amurka ta cimma matsaya da Iran kan shirin kera makamim nukiliya, Trump ya yi bayani

Da yake tsokaci kan hakan, mataimakin ministan wajen Iran, Khatibzadeh ya ce:

“Ya faɗi abubuwa masu karo da juna a cikin magana guda. Ban san ainihin abin da yake nufi ba."
Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House da ke Washington DC Hoto: Pool
Source: Getty Images

Ya ƙara da cewa Iran na ganin yaƙi ba zai haifar da wani sakamako mai kyau ba, amma ƙasar a shirye take ta kare kanta idan aka kai mata hari, kamar yadda NBC News ta kawo.

“Za mu ci gaba da yaƙi har zuwa sojan Iran na ƙarshe idan da bukatar hakan,” in ji shi.

Iran ta musanta ikirarin Shugaba Trump

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta musanta ikirarin cewa ta yarda za ta kwashe gaba daya sindarin Uranium ta mika wa Amurka a wani bangaren na yarjejeniyar sulhu.

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump ya fito ya yi ikirarin cewa Iran ta amince za ta dakatar da duk wani shirinta na nukiliya tare da mika sinadarin Uranium ga Amurka.

Iran ta karyata hakan ta hannun Ma'aikatar harkokin wajen kasar, inda ta ce ba za ta bai wa kowace kasa sindarin, wanda ake hada nukiliya da shi ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262