Lissafi Ya Canza, Iran Ta Tura Sako 'Mara Dadi' zuwa Amurka kan Batun Zaman Sulhu
- Bayanai daga majiyoyi sun nuna cewa har yanzu Iran ba ta amince ta sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka ba
- Rahotanni sun nuna cewa Iran ta aika wannan matsaya zuwa Amurka ta hannun kasar da take shiga tsakani don samar da zaman lafiya watau Pakistan
- Haka zalika, an gano cewa Amurka ta gabatar da wasu sharudda da Iran take ganin sun wuce gona da iri, lamarin da ya sa ta ja baya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Rahotanni sun nuna cewa har yanzu kasar Musulunci ta Iran ba ta amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa da Amurka ba.
Hakan na zuwa ne duk da tayin sake zama da Amurka ta aika wa Iran ta hannun kasar Pakistan, matakin da ake ganin yana neman kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Sulhun Amurka da Iran na tangal-tangal
Wasu majiyoyi da dama sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Tasnim News cewa har yanzu Iran ba ta amince da batun sake komawa teburin sulhu da Amuka ba.
Bayanai sun nuna cewa Iran ta dauki wannan matsaya ne sakamakon matakan da Shugaban Amurka Donald Trump ya ɗauka na kakabawa Iran takunkumin soji a teku.
Idan ba ku manta ba Shugaba Trump ya dauki matakin haka zirga-zirga da duk wata mu'malar kasuwanci a tashohin ruwa na kasar Iran.
Sharuddan Amurka sun yiwa Iran tsauri
Haka zalika rahotonni sun nuna cewa wasu sharudda masu tsauri da Amurka ta gabatar a shirin ci gaba da tattaunawar, sun taka rawa wajen jefa Iran cikin shakku.
Majiyoyin sun ce tattaunawa tsakanin bangarorin biyu na ci gaba ne ta hanyar musayar saƙonni, amma Iran na ganin wasu daga cikin buƙatun Amurka sun wuce gona da iri, cewar tashar Al-Jazeera.
Iran ta bayyana a fili cewa sauya tsauraran sharuddan Amurka shi ne muhimmin sharadi domin ci gaba da tattaunawar, in ba haka ba, ba za ta ɓata lokaci ba a tattaunawa mai tsawo da ba za ta haifar da sakamako mai kyau ba.

Source: Getty Images
Iran ta tura sako ga Amurka
Haka kuma, rahoton ya ce Iran ta isar da wannan matsaya ga jami’an Amurka ta hannun ƙasar Pakistan, wadda ke taka rawa a matsayin mai shiga tsakani a rikicin.
Har yanzu ana ganin kasashen za su cimma matsayar komawa birnin Islamabad don ci gaba da tattaunawa gaba da gaba, amma dai babu tabbacin ranar da za su sake zama a yanzu.
Iran ta yi fatali da kalaman Trump kan Uranium
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Musulunci ta Iran ta musanta labarin cewa ta amince za ta kwashe duka sindarin Uranium dinta ta mika wa Amurka.
Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce hakan ba zai taba yiwuwa ba, domin ba za ta mika wa kowace kasa wannan sindari da ake amfani da shi wajen kera makamin nukiliya ba.
Ta kuma ƙara da cewa batutuwan dage takunkumi da kuma biyan diyya kan asarar da aka yi a yaƙi na daga cikin muhimman abubuwan da Iran ke nema a tattaunawar sulhu da Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

