Ba Tsoro: Gargadin da Tawagar Iran Ta Yi Wa Amurka yayin Tattaunawa a Pakistan
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya tuna baya kan abin da ya faru yayin tattaunawa da Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ghalibaf ya bayyana cewa shi da kansa ya gargadi tawagar Amurka gaba da gaba kan mashigar ruwa ta Hormuz
Shugaban majalisar dokokin ya bayyana cewa gargadin ya tilastawa tawagar Amurka sanyawa jirgin ruwan kasar ya koma baya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Birnin Tehran, Iran - Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana wani abu da ya faru yayin tattaunawa da Amurka.
Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa shi da kansa ya gargaɗi tawagar Amurka a Islamabad game da ta’azzara rikici a mashigar ruwa ta Hormuz.

Source: Getty Images
Tashar Press tv ta ce Ghalibaf ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka fitar a ranar Asabar, 18 ga watan Afirilun 2026.
Wane gargadi Iran ta yi wa Amurka?
Ghalibaf ya ce ya gargaɗi tawagar Amurkar da ta zo babban birnin Pakistan don tattaunawar tsagaita wuta cewa dakarun Iran za su buɗe wuta kan jiragen kwashe nakiyoyi idan har suka matsa ko da "inci ɗaya" daga inda suke a wannan muhimmiyar hanyar ruwa.
Babban ɗan majalisar dokokin na Iran kuma jagoran tattaunawa ya bayar da cikakken bayani kan taho-mu-gama da aka yi tsakanin dakarun sojan ruwan Iran da sojojin Amurka a mashigar Hormuz.
Ghalibaf ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da cikakken iko a kan mashigar Hormuz kuma tuni ta tilastawa Amurka ja da baya.
"Na gayawa tawagar Amurka cewa idan jirginsu na kwashe nakiyoyi ya motsa ko da kaɗan daga inda yaje tabbas za mu bude masa wuta."
- Mohammad Bagher Ghalibaf
Jirgin Amurka ya juya baya
Shugaban majalisar dokokin ya ƙara da cewa tawagar Amurkar ta nemi tsawon mintuna 15 domin isar da umarnin cewa jirgin ya juya baya.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Iran ta sake kunyata Trump a idon duniya ana shirin sake zaman sulhu
Ghalibaf ya ƙara da cewa rundunar sojan ruwa ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) ta dakile wani yunƙuri na gudanar da aikin kwashe nakiyoyi, wanda ya ce ya saɓawa yarjejeniyar tsagaita wuta.
"Mun ci gaba har zuwa ga gabar da za a yi arangama, amma sai makiyi ya ja da baya."
- Mohammad Bagher Ghalibaf
Iran za ta ci gaba da iko da mashigar Hormuz
Kakakin majalisar dokokin ta Iran, wanda ya jagoranci tawagar Iran don tattaunawa da tawagar Amurka a Islamabad a makon da ya gabata, ya ce mashigar Hormuz tana ƙarƙashin ikon Jamhuriyar Musulunci ne.
Ya kuma yi watsi da matakin baya-bayan nan na gwamnatin Trump na "killace tashoshin ruwan Iran" a mashigar Hormuz, inda ya kira shi a matsayin "shawara ta sakaci da aka ɗauka cikin jahilci."

Source: Twitter
"Ba zai yiwu wasu su riƙa wucewa ta mashigar Hormuz ba amma mu a hana mu. Idan Amurka ba ta janye killacen ba, lallai zirga-zirga a mashigar Hormuz za ta fuskanci takunkumi."
"Idan har ana yin wata zirga-zirga a mashigar a yau, to ikon mashigar yana hannunmu ne."
- Mohammad Bagher Ghalibaf

Kara karanta wannan
Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz
Jagoran Iran ya aika da sako
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya yabawa dakarun sojojin kasar.
Mojtaba Khamenei ya jinjinawa dakarun ne saboda jarumtakar da suka nuna wajen kare ƙasar a yaƙin da aka tilastawa kasar.
Jagoran ya kuma karrama daukacin kwamandojin da suka jagoranci rundunar sojojin Iran a cikin shekaru 50 da suka gabata.
Asali: Legit.ng
