Yakin Iran da Amurka: Kasashen Turai za su shiga gagarumar matsala nan da mako 6

Yakin Iran da Amurka: Kasashen Turai za su shiga gagarumar matsala nan da mako 6

  • Hukumar makamashi ta Duniya ta yi gargaɗin cewa Turai na da ragowar man jirgi na makonni shida kacal sakamakon toshe mashigar Hormuz
  • Kusan kashi saba'in da biyar na man fetur ɗin jiragen sama da Turai ke amfani da shi yana fitowa ne daga yankin Gabas ta Tsakiya, ga shi a rufe Hormuz
  • Idan ba a buɗe mashigar tekun ba nan ba da daɗewa ba, kamfanonin jiragen sama za su fara soke zirga-zirga a lokacin da aka fara hutun bazara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Faransa – Shugaban Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA), Fatih Birol, ya yi gargaɗin cewa nahiyar Turai za ta fuskanci ƙarancin man fetur ɗin jiragen sama nan da mako shida masu zuwa.

Wannan matsalar za ta zama barazana ga harkokin sufurin jiragen sama, musamman a daidai lokacin da ake shirin fara hutun bazara, muddin aka ci gaba da toshe hanyoyin samar da mai sakamakon yaƙin Iran.

Kara karanta wannan

A karon farko bayan bude Hormuz, an hango jirgin mai na wuce wa ta Iran

Ana fargabar kasashen Turai za su rasa man jiragen sama nan da makonni 6
Wani jirgin Easy ya na shan mai a yayin da zai yake shirin tashi a filin jirgin Southend, Ingila. Hoto: Dan Kitwood/Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin rufe mashigar Hormuz ga Turai

Birol ya bayyana halin da ake ciki a matsayin "babban rikicin makamashi da duniya ta taɓa fuskanta," inda ya yi kira da a sake buɗe mashigar Hormuz domin ba da damar zirga-zirgar mai da iskar gas, in ji rahoton New York Times.

A cewarsa, idan aka gaza buɗe mashigar Hormuz, nan ba da daɗewa ba za a fara jin labaran soke tafiye tafiyen jiragen sama daga wannan birni zuwa wancan birni sakamakon rashin mai.

Rahoton IEA na watan Afrilu ya nuna cewa Turai za ta fara fuskantar ƙarancin man jirgi na zahiri nan da watan Yuni, koda kuwa nahiyar za ta iya samo rabin man da take buƙata daga wasu wuraren.

Turai na cikin 'halin ƙaka-ni-kayi'

Turai ta dogara kacokan kan Gabas ta Tsakiya, inda yankin ke samar da kusan ganga 375,000 a rana, wanda ya kai kashi 75 cikin ɗari na dukkan man jirgi da Turai ke shigo da shi.

Kara karanta wannan

Ana shirin tafiya Hajji, an fara barazanar tsayar da aiki da jiragen sama a Najeriya

Fatih Birol ya yi amfani da kalmar 'Dire Straits,' wajen bayyana halin ƙaka-ni-kayi da ake ciki, yana mai cewa tsawon lokacin da mashigar za ta shafe a rufe, zai ƙara ta'azzara matsalolin tattalin arziki da hauhawar farashi a faɗin duniya.

Wannan gargaɗin na zuwa ne mako guda bayan da hukumar ACI Europe ta bayyana cewa Turai na da ragowar man makonni uku kacal kafin abubuwa su jagule, kamar yadda rahoton Reuters ya nuna.

Fatih Birol ya ce Turai za ta rasa man jirgin sama nan da mako 6.
Shugaban Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA), Fatih Birol, ya na magana game da makomar makamashin Turai. Hoto: Nicolas TUCAT / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Takun saƙa tsakanin Amurka da Iran

Ƙarancin man sakamako ne kai-tsaye na matakin da Iran ta ɗauka na rufe mashigar Hormuz, wadda ita ce hanyar da kashi 20 cikin ɗari na man fetur ɗin duniya ke bi.

Tehran ta ɗauki wannan mataki ne a matsayin martani ga yaƙin da ake yi, yayin da Amurka ma ta sanya nata takunkumin na toshe jiragen Iran a cikin wannan mako.

Har yanzu ba a san tsawon lokacin da mashigar za ta kasance a rufe ba, duba da cewa tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ta ruguje a ƙarshen makon da ya gabata.

Hormuz: Iran ta farmaki jiragen dakon mai

A wani labari, mun ruwaito cewa, dakarun IRGC na Iran sun buɗe wa jiragen ruwa wuta kusa da ƙasar Oman bayan sake rufe mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Yakin Iran, Amurka: Najeriya da wasu kasashe na iya samun tallafin dala biliyan 50

Hukumomin ruwa na Birtaniya (UKMTO) sun tabbatar da cewa jiragen yaƙi na Iran sun kai hari ba tare da wani gargadi ba da tsakiya ranar Asabar.

Amurka da Iran na ci gaba da takun saƙa yayin da sojojin ruwan Amurka ke gadin jiragen dakon mai don tabbatar da ba su fuskanci harin Iran ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com