Abu Ya Girma: Iyalan Sojoji da Ake Zargi da Juyin Mulki Sun Fadi Halin da Suke Ciki

Abu Ya Girma: Iyalan Sojoji da Ake Zargi da Juyin Mulki Sun Fadi Halin da Suke Ciki

  • Iyalan sojojin da ake tsare da su kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu sun yi magana game da jami'an
  • Sun bukaci a gudanar da shari’a cikin adalci da gaskiya, tare da bai wa sojojin damar ganin lauyoyinsu da ‘yan uwansu
  • A’isha Nana, matar daya daga cikin sojojin, ta ce ba sa adawa da doka, amma suna son a kare hakkin wadanda ake zargi yayin shari’ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Iyalan wasu sojojin da ake tsare da su kan zargin shirya yunkurin kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun dage cewa har yanzu ba a tabbatar da laifinsu ba.

Iyalan sun bukaci a bai wa sojojin damar samun lauyoyinsu da ‘yan uwansu, tare da tabbatar da cewa ana kula da su yadda ya kamata yayin da shari’ar soja ke gudana.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Iyalan sojojin da ake zargi da juyin mulki sun magantu
Sojan da ake zargi da juyin mulki, Kanal Mohammed Ma'aji da Bola Tinubu. Hoto
Source: Facebook

Da take magana a wata hira da yan jarida wanda Premium Times ta bibiya, Nana ta ce iyalan ba sa adawa da bin doka, amma suna son a kare hakkin sojojin.

Juyin mulki: Iyalan sojoji sun yi korafi

A’isha Nana, wadda mijinta yana cikin sojojin da ake zargi, ta ce iyalan suna cikin damuwa game da yadda ake kula da jami’an tun bayan kama su.

Ta ce dole ne a bar tsarin shari’a ya yi aikinsa, amma gwamnati da hukumomin soja su tabbatar ba a azabtar da wadanda ake zargin ba.

Nana ta ce bai dace a hana sojojin ganin ‘yan uwansu ko lauyoyinsu ba, domin hakan na iya tauye musu hakkinsu na samun kariya ta doka.

Ta kuma ce bayan kama sojojin, iyalansu ba su samu wata sanarwa ta hukuma daga rundunar sojin Najeriya ba game da zarge-zargen da ake yi musu.

Maimakon haka, Nana ta ce iyalan ne suka fara jin labarin zarge-zargen ta kafafen yada labarai bayan an wallafa rahotannin lamarin.

Kara karanta wannan

Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Ta ce ba su samu wata sanarwa ko sadarwa kai tsaye daga rundunar soja ba, sai dai abin da suka gani a kafafen yada labarai.

Nana ta kuma yi watsi da ra’ayin cewa sojojin da ake zargi da juyin mulki sun gaya wa matansu wani shirin kifar da gwamnati.

A cewarta, jami’an soja ba sa yawan tattauna irin wadannan batutuwa masu matukar muhimmanci da sirri da matansu ko iyalansu.

Ta ce ya kamata zarge-zargen su kasance da hujjoji, sannan a gabatar da su gaban tsarin shari’a na gaskiya da bude ido.

Ta ce:

“Har yanzu ba a tabbatar da laifinsu ba.”
Ana ci gaba da shari'a kan sojojin da ake zargi da juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu da aka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: UGC

Bukatar iyalana ga kotu a Najeriya

Nana ta ce hukumomi su gabatar da duk wata hujja da suke da ita, sannan a bar kotu ta yanke hukunci kan ko sojojin suna da laifi ko ba su da shi.

Matar sojan ta kuma bayyana damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin jinkirin gurfanar da jami’an da ake zargi a gaban kotu.

Ta ce iyalan da kansu sun bukaci a gurfanar da sojojin bisa ka’ida, tare da gudanar da shari’ar cikin fili domin jama’a su fahimci abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano dandazon 'yan bindiga da tsakar rana, suna shirin afkawa Katsina

Sai dai ta yi zargin cewa ba a bar wasu daga cikin ‘yan uwan sojojin su halarci zaman kotun ba.

Nana ta kuma ce an takaita sadarwa tsakanin wasu daga cikin sojojin da ake zargi, lauyoyinsu da iyalansu, lamarin da ya kara jefa iyalan cikin damuwa.

Ta ce babban abin da iyalan suke bukata shi ne a gudanar da shari’ar cikin adalci, gaskiya da kuma bayyananniyar hanya.

An gano yadda Tinubu ya sha da kyar

An ji cewa masu bincike kan zargin yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun gano manhajojin da aka yi amfani da su.

Rahoto ya nuna cewa wasu da ake zargi da hannu a shirin juyin mulkin 2025 sun yi amfani da WhatsApp da Zangi wajen sadarwa.

Kanal Mohammed Ma’aji ne ya gabatar da Zangi ga wasu daga cikin mutanen da ake bincike a kansu domin gano gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.