Kasar Iran Ta Amince Ta Mika Sindarin Kera Nukiliya ga Amurka? Gaskiya Ta Bayyana

Kasar Iran Ta Amince Ta Mika Sindarin Kera Nukiliya ga Amurka? Gaskiya Ta Bayyana

  • Kasar Iran ta musanta ikirarin cewa ta yarda za ta kwashe gaba daya sindarin Uranium ta mika wa Amurka a wani bangaren yarjejeniyar sulhu
  • Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce hakan ba zai taba yiwuwa ba, domin ba za ta mika wa kowace kasa wannan sindari ba
  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce jami’an Iran sun amince da dukkan sharuɗɗa, ciki har da fitar da uranium daga ƙasar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Gwamnatin Musulunci ta Iran ta musanta labarin cewa ta amince za ta kwashe duka sindarin Uranium dinta ta mika wa Amurka a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya.

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump ya fito ya yi ikirarin cewa Iran ta amince za ta dakatar da duk wani shirinta na nukiliya tare da mika sinadarin Uranium ga Amurka.

Kara karanta wannan

Tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta dawo farko, an ji halin da ake ciki

Shugaban Iran.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian lokacin da ya halarci taron manema labarai na farko bayan ya hau mulki a 2024 a Tehran Hoto: Majid Saedi
Source: Getty Images

Iran za ta mika sindarin Uranium ga Amurka?

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa Iran ta karyata hakan ta hannun Ma'aikatar harkokin wajen kasar, inda ta ce ba za ta bai wa kowace kasa sindarin, wanda ake hada nukiliya da shi ba.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana cewa Iran ba za ta taba fitar da sinadarin Uranium ɗin da ta tace zuwa wata ƙasa ba a kowane hali.

Baghaei ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na ƙasar, inda ya jaddada cewa batun mika uranium ga Amurka bai taɓa zama wani zaɓi ba.

“Iran ba za ta taba mika uranium ɗinta zuwa wani wuri ba. Kamar yadda ƙasar Iran take da girma da kima a gare mu, haka ma wannan uranium ɗin yake,” in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa batutuwan dage takunkumi da kuma biyan diyya kan asarar da aka yi a yaƙi na daga cikin muhimman abubuwan da Iran ke nema a tattaunawar sulhu da Amurka.

Kara karanta wannan

Amurka ta cimma matsaya da Iran kan shirin kera makamim nukiliya, Trump ya yi bayani

Abin da Sshugaban Amurka ya fada

Tun farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa CBS News cewa jami’an Iran sun amince da dukkan sharuɗɗa, ciki har da fitar da uranium daga ƙasar.

Trump ya ce:

"Mutanenmu tare da Iran za su yi aiki tare don kwashe uranium ɗin, sannan za mu kai shi Amurka.”
Shugaban Amurka.
Shugaban kasa, Donald Trump na magana a taron da aka shirya kan wani kudiri a Las Vegas Hoto: Win Macnamee
Source: Getty Images

Sai dai kalaman na Trump sun ci karo da matsayar gwamnatin Iran, wadda ta dage cewa babu wani rudani a matsayarta.

“Mun bayyana matsayinmu karara, babu wani ɓoye-ɓoye a tattaunawar,” in ji Baghaei.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin tsakanin Amurka da Iran kan shirin nukiliya na Tehran na ci gaba da zama babban ƙalubale, duk da ƙoƙarin diflomasiyya da ake yi domin cimma yarjejeniya mai dorewa.

Sulhun Amurka da Iran na matakin farko

A baya, an ji cewa tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Jamhuriyar musulunci ta Iran na nan a matakin farko, inda a yanzu ake kokarin shimfida ka’idoji.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

Wata majiya daga Iran ta bayyana cewa matakai na gaba da za a dauka tsakanin Iran da Amurka za su mayar da hankali ne kan amincewa da tsarin yadda za a gudanar da tattaunawa.

Majiyar ta ce duk da wannan ci gaba da aka samu tsakanin kasashen biyu, har yanzu kokarin sulhun da ake yi na nan a matakin farko.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262