Wata Sabuwa: Iran Ta Sake Kunyata Trump a Idon Duniya ana Shirin Sake Zaman Sulhu

Wata Sabuwa: Iran Ta Sake Kunyata Trump a Idon Duniya ana Shirin Sake Zaman Sulhu

  • Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi martani mai zafi ga Shugaba Donald Trump na Amurka
  • Ghalibaf ya bayyana cewa Trump ya shararo wasu karairayi guda bakwai a cikin bayanan da ya yi na baya-bayan nan
  • Shugaban majalisar dokokin ya bayyana cewa karya ba ta taimaki Amurka ba a lokacin yaki, kuma ba za ta taimake ta ba a lokacin tattaunawa

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi martani ga Shugaba Donald Trump kan ikirarin da ya yi na baya-bayan nan.

Mohammad Bagher Ghalibaf ya ƙaryata dukkan iƙirarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi game da mashigar ruwa ta Hormuz.

Iran ta musanta ikirarin da Trump ya yi
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a wani rubutu da Shugaban majalisar dokokin ta Iran ya yi a shafinsa na X a ranar Juma'a, 17 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Shugaba Donald Trump ya fadi sharadin da Iran ta amince da shi ana shirin sake zama

Mohammad Bagher Ghalibaf ya bayyana cewa Trump ya yi ikirari guda bakwai, kuma dukkaninsu karya ne.

Donald Trump ya yi ikirari kan Hormuz

Wannan martani ya zo ne bayan da Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social cewa Iran ta "amince ba za ta sake rufe mashigar Hormuz ba har abada."

Trump ya kuma yi iƙirarin cewa killace hanyoyin ruwan Iran da Amurka ke yi zai ci gaba da kasancewa har sai an kammala tattaunawa, inda ya ƙara da cewa tattaunawar tsagaita wuta za ta kammala "cikin sauri" domin an riga an tattauna yawancin batutuwa.

Wane martani kasar Iran ta yi?

A martanin da ya yi, Mohammad Bagher Ghalibaf ya rubuta cewa:

"Shugaban Amurka ya yi iƙirari bakwai a cikin sa'a ɗaya, kuma dukkan waɗannan iƙirari bakwai ɗin ƙarya ne."

Ghalibaf ya nanata cewa Iran za ta kulle mashigar Hormuz idan har aka ci gaba da killace tashoshin ruwanta.

"Idan har killace hanyoyin ruwanmu ya ci gaba, to mashigar Hormuz ba za ta kasance a buɗe ba."

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

- Mohammad Bagher Ghalibaf

Ya kuma jaddada cewa zirga-zirga ta mashigar Hormuz za ta kasance ne kawai ta hanyar da aka ware kuma tare da "izini daga Iran."

"Ko mashigar za ta kasance buɗe ko a rufe, da kuma ƙa'idodin da za su kiyaye ta, fagen fama ne zai tabbatar da su, ba shafukan sada zumunta ba."

- Mohammad Bagher Ghalibaf

Ghalibaf ya karyata ikirarin Trump
Mohammad Bagher Ghalibaf a cikin jirgi lokacin tafiya zuwa tattaunawa a Pakistan Hoto: @mb_ghalibaf
Source: Twitter

Ghalibaf ya ja kunnen Amurka

Ghalibaf ya bayyana cewa yin amfani da "ƙarya" bai taimaki Amurka ba lokacin da take kai hare-hare, kuma ba za su taimaka mata ba yayin tattaunawa.

Ya ce yaƙin juya ra'ayin jama'a babban ɓangare ne na yaƙi, amma al'ummar Iran ba za su taba yarda a yaudaresu da irin waɗannan dabarun ba.

Ghalibaf ya buƙaci jama'a da su duba hirar baya-bayan nan da kakakin ma'aikatar wajen Iran ya yi domin samun ingantattun bayanai kan halin da tattaunawar take ciki, maimakon bin jita-jitar Amurka.

Iran ta yi fatali da tsagaita wutar wucin gadi

Kara karanta wannan

Ana shirin sake zama, Trump ya fadi abin da zai harzuka Jamhuriyar Musulunci ta Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matsayarta kan tattaunawar da ake yi da Amurka.

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ya bayyana cewa kasarsa ba za ta amince da duk wani tsagaita wuta na wucin gadi ba.

Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa Iran na son a kawo karshen yakin gaba daya a yankin Gabas ta Tsakiya da ake kai wa hari ɗaya bayan ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng