Bayan Ta Kekashe Kasa, Amurka Ta Gabatar da Sabon Tayi ga Kasar Musulunci Ta Iran
- Yayin da Iran ta dage cewa ba za ta koma teburin tattaunawa ba, Amurka ta fara kokarin shawo kanta domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya
- Iran ta bayyana cewa ta karbi sababbin sharudda daga Amurka a yan kwanakin nan kuma tuni ta fara duba da nazari a kansu
- Ana sa ran dai wannan tayi zai sa Iran ta sassauta matsayarta bayan ta yanke shawarar ba za ta koma zaman sulhu ba sai an fitar da tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Iran ta bayyana cewa tana nazarin sababbin sharudda da Amurka ta gabatar mata a tattaunawar da ke gudana ta hanyar tura sakonni.
Sai dai duk da Amurka ta canza sharuddan, gwamnatin kasar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa ba za ta yi wani sassauci ba kan manyan muradunta.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Kasar Musulunci ta Iran ta jikawa Amurka aiki ana shirin komawa teburin sulhu

Source: Facebook
Amurka ta gabatar da sabon tayi ga Iran
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da Kwamitin Tsaron Ƙasa na Iran ya fitar ranar Asabar, 18 ga watan Afrilun 2026, kamar yada tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Sanarwar ta ce Amurka ta gabatar da sabon tayi mai kunshe da sharudda daban-daban a ‘yan kwanakin nan, amma har yanzu Tehran na duba su kuma ba ta yanke hukunci ba.
Sanarwar ta kuma nuna cewa babban hafsan rundunar sojin Pakistan ya kai ziyara Tehran domin taka rawa a matsayin mai shiga tsakani, bayan da tattaunawar farko a Islamabad ta ƙare ba tare da cimma yarjejeniya ba.
Yadda Iran ta dage kan muradunta
A baya-bayan nan, jami’an Iran sun bayyana cewa ba za a sanya ranar sabon zagayen tattaunawa ba har sai an amince da tsarin da za a bi.
Mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Saeed Khatibzadeh, ya jaddada cewa dole ne kowace yarjejeniya ta kare haƙƙin Iran ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan
Lissafi ya canza, Iran ta tura sako 'mara dadi' zuwa Amurka kan batun zaman sulhu
Haka kuma, Iran ta nuna damuwa kan abin da ta kira tsauraran buƙatu daga Amurka, inda ta bayyana cewa janye irin waɗannan buƙatu na daga cikin sharudan da za su ba da damar ci gaba da tattaunawa.
Rahotanni sun ce Tehran ta isar da wannan matsaya ga Washington ta hannun Pakistan, wadda ke taka muhimmiyar rawa a matsayin mai shiga tsakani.

Source: Getty Images
Iran za ta koma tattaunawa da Amurka?
Sai dai bayan haka, gwamnatin Iran ta tabbatar da cewa ta karbi sabon tayi daga Amurka, kuma tana nazari kansu kafin ta yanke hukunci, kamar yadda Ahram News ta ruwaito.
Ana sa ran dai wannan ta yi zai sa Iran ta sauko kuma ta amince da bukatar komawa zagaye na biyu na tattaunawar sulhu a birnin Islamabad.
Wane mataki ake a tattaunawar sulhu?
An ji cewa rahotanni daga kasar Musulunci ta Iran sun nuna har yanzu ba a je ko'ina ba a tattaunawar da kasar ta fara da Amurka.
Wata majiya daga Iran ta bayyana cewa matakai na gaba da za a dauka tsakanin Iran da Amurka za su mayar da hankali ne kan amincewa da tsarin yadda za a gudanar da tattaunawar ta gaba.
Majiyar ta ce har yanzu bangarorin biyu na kan matakin farko ne na tattaunawa, inda ake kokarin shimfida ka’idojin da za su jagoranci zaman sulhu.
Asali: Legit.ng