A Karon Farko bayan Bude Hormuz, An Hango Jirgin Mai na Wuce wa Ta Iran
- Jirgin kasuwa na farko ya ratsa ta mashigar Hormuz bayan makonni na rufe hanyar sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya
- Iran ta sanar da sake buɗe hanyar ga dukkanin jiragen kasuwanci bayan an fara tattaunawa kawo karshen yaƙin
- Matakin ya biyo bayan tsagaita wuta na kwanaki 10 da tattaunawar sulhu tsakanin Iran da Amurka wanda Pakistan ta shiga tsakani
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Iran – Jirgin farko ya ratsa mashigar Hormuz bayan bude hanya a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu na shekarar 2026 da Iran ta yi.
Jirgin mai suna Celestyal Discovery ya ratsa mashigar ne ‘yan awanni kaɗan bayan ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya tabbatar da bude hanya ga dukkanin jiragen kasuwanci.

Kara karanta wannan
Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Iran ta yi barazanar kai hari ga duk wani jirgi da zai bi ta wannan hanya sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakaninta da Amurka da Isra’ila.
An buɗe mashigar Hormuz
New York Post ta wallafa cewa bayanan zirga-zirgar jiragen ruwa sun nuna cewa jirgin ya tashi daga tashar Port Rashid da ke Dubai da 11.36 na safe a agogon yankin.
Hakan ya sa ya zama jirgin fasinja na farko da ya bar yankin tun bayan fara rikicin da aka fara a ranar 28 ga watan Fabarairu na shekarar 2026.
An ruwaito cewa jirgin, wanda ke iya ɗaukar fasinjoji kusan 1,360, ba ya ɗauke da kowa a lokacin da ya ratsa mashigar.
Yanzu haka yana kan hanyarsa ta zuwa Muscat a ƙasar Oman, inda ake sa ran zai isa da yammacin ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu na shekarar 2026.
Ana ƙoƙarin sulhu a Iran
Jirgin na daga cikin jiragen ƴan kasuwa da dama da suka makale a Tekun Faha ko kuma aka tilasta masu soke tafiye-tafiyensu bayan rikicin ya ɓarke a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
A wancan lokaci, Iran ta yi barazanar kai hari ga duk wani jirgi da zai bi mashigar lamarin da ya sa harkokin kasuwanci suka tsaya cak a yankin.
Yayin da rikicin ke ƙara ƙamari a Gabas ta Tsakiya, Iran ta kuma cika hanyar da abubuwa masu fashewa tare da jaddada gargadin cewa duk jirgin da zai wuce ba tare da izini ba zai fuskanci hari.

Source: Getty Images
Har ma an ambaci yiwuwar tilasta wa jiragen biyan kuɗin haraji masu yawa kafin su ratsa hanyar idan suna son wuce wa lami lafiya.
Sai dai a yanzu, bayan da Amurka da Iran ke ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya, tare da amincewa da tsagaita wuta na kwanaki 10, hukumomin Iran sun ce an buɗe hanya na wannan lokaci.

Kara karanta wannan
Iran ta kafe kan sharadin sulhu da Amurka, ta yi fatali da tsagaita wuta na wucin gadi
Masu sa ido na ganin cewa wannan mataki na iya taimakawa wajen farfaɗo da harkokin sufuri da kasuwanci a yankin, musamman ganin muhimmancin mashigar Hormuz wajen jigilar mai da sauran kayayyaki zuwa sassa daban-daban na duniya.
Iran ta yi magana kan sulhu
A baya, mun wallafa cewa Iran ta ce ba za ta amince da tsagaita wuta na dan lokaci ba yayin da Amurka da Isra'ila ke hararar ƙasashen shiyyar ana kai hare-hare.
An fara tattauna wannan batu ne jim kadan bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ana dab da cimma matsaya wajen kawo karshen yakin.
Iran ta zargi Amurka da Isra’ila da haddasa rashin zaman lafiya a yankin Iran ta dage kan kawo karshen yaki gaba daya, ba wai a tsaya na wani lokaci kuma a ɗora ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
