Jami'ar ABU Ta Waiwayi Farfesa Abdullahi, Wanda Aka Ce Yana da PhD 5, MSc 5 da Digiri 7

Jami'ar ABU Ta Waiwayi Farfesa Abdullahi, Wanda Aka Ce Yana da PhD 5, MSc 5 da Digiri 7

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

  • Mahukunta a Jami'ar ABU Zaria sun fara gudanar da bincike kan jerin takardun karatun Farfesa Abdullahi Abubakar
  • A baya-bayan nan dai rahotanni sun ce malamin jami’ar na da digirin PhD biyar, MSc guda biyar da sauran takardun karatu
  • Jami’ar ABU ta ce ba za ta yi gaggawar yanke hukunci kan lamarin ba kafin kammala binciken

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ta fara daukar matakan gano gaskiyar bayanan karatun daya daga cikin malamanta, Farfesa Abdullahi Abubakar bayan tarihin karatunsa ya jawo hankalin jama’a a Najeriya.

Jami’ar ABU Zaria ta ce tana sane da wani bayani da ke yawo a kafafen sada zumunta kan cancantar malamin, kuma za ta bayyana matsayinta ga jama’a bayan kammala binciken da ya dace.

ABU Zaria.
Kofar shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria (ABU) Hoto: ABU Zaria
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa daraktan yada labarai na ABU, Awwal Umar, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce jami’ar za ta yi magana a lokacin da ya dace bayan an tabbatar da gaskiyar lamarin.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Jami'ar ABU ta fara bincike

Awwal ya bayyana cewa jami’ar ba za ta yi gaggawar yanke hukunci kan batun ba, domin akwai bukatar kammala binciken da ake gudanarwa kafin a fitar da matsaya ta hukuma.

Ya ce jami’ar za ta bi dukkan hanyoyin da suka dace domin tantance sahihancin bayanan da ake yadawa kan takardun karatun Farfesa Abdullahi Abubakar.

Matakin na jami’ar ya biyo bayan wasu rahotanni da bayanai da suka fara yaduwa a kafafen sada zumunta, inda aka bayyana yawan digirin da malamim ya yi a tarihin karatunsa.

An ce yana da digirin PhD 5

Rahotannin da suka jawo ce-ce-ku-ce sun nuna cewa bayanan karatun Farfesa Abubakar sun hada da digirin PhD guda biyar, digiri na biyu (MSc) biyar, digiri bakwai da difloma 11, baya ga wasu takardun karatu.

Yawan takardun karatun da aka danganta da malamin ya jawo tambayoyi musamman saboda matsayinsa na farfesa a jami’ar da kuma irin ayyukan da yake gudanarwa a fannonin koyarwa da bincike.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, tsohon antoni janar ya riga mu gidan gaskiya

Sai dai ABU ba ta tabbatar da sahihancin rahotannin ba, inda ta jaddada cewa tana bukatar gudanar da cikakken bincike kafin ta bayyana matsayinta, cewar rahoton Aminiya.

Abdullahi Abubakar.
Malamim jami'ar ABU, Farfesa Abdullahi Abubakar Hoto: Usman Abba Magaji
Source: Twitter

Farfesan bai yi cikakken bayani ba

Kokarin samun cikakken bayanin Farfesa Abdullahi Abubakar kan batun bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Sai dai lokacin da aka tura masa sakon waya domin neman jin ta bakinsa, malamin ya nuna cewa ya ga abubuwan da ke faruwa amma bai shirya yin magana kan batun a yanzu ba.

Amsar da ya bayar a sakon ta kasance:

“Na karbi sakonku kuma na lura da shi, amma ba yanzu ba. Na gode.”

ABU ta fara digirin Hajji da Umrah

A wani labarin, kun ji cewa jami'ar Ahmadu Bello da NAHCON sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ƙaddamar da digirin MBA kan gudanar da harkokin Hajji da Umrah.

Shirin haɗin gwiwar zai haɗa da koyarwa, bincike, horaswa, ƙwarewar aiki da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa domin inganta harkokin gudanar da Hajji

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262