Iran Ta Nuna wa Trump Yatsa, Ta Bude Wuta kan Wasu Jirage da Suka Shiga Hormuz

Iran Ta Nuna wa Trump Yatsa, Ta Bude Wuta kan Wasu Jirage da Suka Shiga Hormuz

  • Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun buɗe wa jiragen ruwa wuta kusa da ƙasar Oman bayan sake rufe mashigar Hormuz
  • Hukumomin ruwa na Birtaniya (UKMTO) sun tabbatar da cewa jiragen yaƙi na Iran sun kai hari ba tare da wani gargadi ba da tsakiya ranar Asabar
  • Amurka da Iran na ci gaba da takun saƙa yayin da sojojin ruwan Amurka ke gadin jiragen dakon mai don tabbatar da ba su fuskanci harin Iran ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran – Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta buɗe wa aƙalla jirgin ruwa ɗaya wuta a yankin tekun Oman a ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026.

Wannan mataki ya biyo bayan sake sanar da rufe mashigar Hormuz da Tehran ta yi, kamar yadda hukumar kula da harkokin kasuwancin teku ta Birtaniya (UKMTO) ta bayyana.

Kara karanta wannan

A karon farko bayan bude Hormuz, an hango jirgin mai na wuce wa ta Iran

Iran ta farmaki wasu jirage da suka shiga Hormuz
Wani jirgin dakon mai a mashigar ruwan Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta farmaki jirage a Hormuz

Rahoton New York Times ya nuna cewa jiragen yaƙi biyu na Iran sun bi sahun wani jirgin dakon mai, daga tazarar mil 20 da gabar tekun Oman, inda suka buɗe wa jirgin wuta ba tare da wani gargadi ba.

Bayan sa'o'i biyu, an sake kai wa wani jirgin daban hari da wani abu da ba a san ko mene ne ba, wanda ya lalata wasu rumbunan adana mai da ke kan jirgin, amma bai haddasa gobara ko gurɓata muhalli ba.

Harin na ranar Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026, ya tilasta wa aƙalla jiragen ruwa biyu na ƙasar Indiya komawa baya don gudun harin Iran.

Ɗaya daga cikin waɗannan jiragen babban jirgin dakon mai ne na (VLCC) wanda ke ɗauke da gangar danyen mai har miliyan biyu daga ƙasar Iraki.

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

Wannan lamari ya jefa harkokin kasuwancin man fetur na duniya cikin fargaba, duba da cewa kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur ɗin da ake amfani da shi a duniya yana ratsawa ne ta wannan matsatsiyar mashiga.

Iran ta bayyana cewa ta sake rufe mashigar ne saboda Amurka ba ta janye takunkumin da ta sanya wa tashoshin jiragen ruwan ta ba, in ji rahoton CNN.

Rundunar haɗin gwiwa ta sojin Iran ta sanar a ranar Asabar cewa "ikon mashigar Hormuz ya koma hannun sojojin Iran," inda suka yi gargaɗin cewa babu jirgin da zai wuce sai idan ya nemi izini kuma ya biya haraji ga hukumar ruwan Iran.

Rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta mayar da martani ta hanyar yaɗa hotunan jiragen yaƙi da masu saukar ungulu da aka tura tsaron yankin domin tabbatar da ƴancin zirga-zirga.

Iran ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz duk da cewa Trump ya yi mata barazana.
Shugaban Amurka, Donald Trump (hagu) da Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi (dama) Hoto: Anna Moneymaker / ATTA KENARE via Getty Images
Source: Getty Images

Fargabar ci gaban yakin Iran da Amurka

Tun bayan da tattaunawar diflomasiyya ta gaza a farkon wannan mako, sojojin ruwan Amurka suka fara kare jiragen dakon mai, yayin da sojojin Iran ke ƙoƙarin nuna ikon su a kan jiragen da za su wuce.

Wannan rikici, wanda ya barke tun a ƙarshen watan Fabrairu, 2026 ya haifar da hare-hare da dama kan jiragen kasuwanci ta hanyar amfani da jirage mara matuƙi da makami mai linzami.

Kara karanta wannan

Trump: A karo na 4, majalisar Amurka ta sake kuri'a kan yaƙi da Iran

A halin yanzu, CENTCOM ta bayyana cewa ta riga ta mayar da jiragen Iran har guda 21 gida tun farkon fara wannan takun saƙa a ranar Litinin.

Iran ta ki yarda ta sake tattaunawa da Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, har yanzu kasar Musulunci ta Iran ba ta amince da gudanar da sabon zagayen tattaunawa da Amurka ba.

Hakan na zuwa ne duk da tayin sake zama da Amurka ta aika wa Iran ta hannun kasar Pakistan, matakin da ake ganin yana neman kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Iran ta bayyana a fili cewa sauya tsauraran sharuddan Amurka shi ne muhimmin sharadi domin ci gaba da tattaunawar, in ba haka ba, ba za ta ɓata lokaci ba a tattaunawa mai tsawo da ba za ta haifar da sakamako mai kyau ba. Read more:

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com