Ana Maganar Sulhu, Trump Ya Yi Barazanar Sake Sakin Bama Bamai a Iran

Ana Maganar Sulhu, Trump Ya Yi Barazanar Sake Sakin Bama Bamai a Iran

  • Tattaunawar kai tsaye tsakanin kasashen Amurka da Iran da aka fara a Pakistan a karshen makon da ya gabata ba ta kai ga matsaya ba har yanzu
  • Duk da rahotanni sun nuna cewa akwai abubuwan da suka hadu a kai, kasashen biyu sun kasa cimma daidaito kan shirin nukiliyar Iran da wasu batutuwa
  • Yayin hira da 'yan jarida, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi barazanar sake kai hare-haren bama-bamai Iran idan tattaunawa ta ci tura

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Iran ta ce ta bude mashigar Hourmuz gaba daya ga jiragen ruwa na kasuwanci, amma har yanzu akwai tambayoyi kan yadda jiragen ke iya wucewa cikin ‘yanci.

An nuna shakku kan batun ne ganin cewa Tehran na ci gaba da rike ikon tantance wadanda za su wuce, tare da yin barazanar sake rufe mashigar idan Amurka ta ci gaba da kakaba takunkumi kan jiragen ruwanta da tashoshinta.

Kara karanta wannan

Amurka ta cimma matsaya da Iran kan shirin kera makamim nukiliya, Trump ya yi bayani

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump da wajen da aka kai hari Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A gefe guda kuma, Al-Jazeera ta rahoto cewa Donald Trump ya ce a shirye suke su cigaba da kai hare-hare idan tattaunawar ta gaza kaiwa ga yarjejeniya.

Donald Trump zai kai farmaki Iran

Da yake amsa tambaya daga wani dan jarida a daren Juma’a kan abin da zai yi idan ba a cimma yarjejeniya ba kafin tsagaita wutan ya kare a mako mai zuwa.

ND TV ta rahoto Trump ya ce:

“Ban sani ba… amma watakila ba zan kara wa’adin ba, don haka zan cigaba da kakaba takunkumi, kuma za mu sake bama-bamai.”

Sai dai ya kuma shaida wa manema labarai da ke tare da shi a cikin jirgi zuwa Washington cewa yarjejeniya “za ta tabbata,” kuma ya yi watsi da yiwuwar Iran ta kakaba haraji ko wasu abubuwa na daban kan mashigar Hourmuz.

Takun saka tsakanin Iran da Trump

Tun da farko, a ranar Juma'a, Trump ya yi maraba da sanarwar Iran, inda ya sanar da cewa Tehran ta bude mashigar Hormuz gaba daya kuma a shirye take domin zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

Amma bayan mintuna kadan, ya sake wallafa cewa takunkumin rundunar ruwan Amurka zai ci gaba:

“Har sai mun kammala yarjejeniyarmu da Iran 100 bisa 100.”
Shugaba Donald Trump
Donald Trumo yana yi wa Amurkawa jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce jiragen ruwa za su bi hanyoyin da Jamhuriyar Musulunci ta tsara tare da hadin gwiwa da hukumomin Iran, wanda ke nuna cewa kasar na shirin ci gaba da rike wani iko a kan mashigar.

Jami’an Iran sun ce takunkumin ya saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a makon da ya gabata tsakanin Iran da Amurka.

Dangote ya magantu a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa attajirin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya fadi wasu abubuwa da suka hana ruwa gudu a nahiyar Afrika.

Dangote ya bayyana cewa akwai wasu 'yan kasashen waje da ke dakile cigaba a Afrika saboda kare muradunsu a wani taro a Amurka.

Duk da matsalolin da ya ambata, Dangote ya bukaci 'yan Afrika su tashi tsaye domin magance damuwowinsu ta hanyar zuba jari a nahiyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng