Yaƙin Amurka: Bayan Hormuz, Ƙawayen Iran na Barazanar Rufe Wata Babbar Mashigar Ruwa
- Wani jami’i a gwamnatin ‘yan Houthis ya yi barazanar rufe mashigar Bab al-Mandeb idan manufofin Donald Trump suka ci gaba
- Hussein al-Ezzi ya ce idan Sanaa ta rufe mashigar, babu wanda zai iya sake bude ta, yana kira a dakatar da manufofin da ke hana zaman lafiya
- Mashigar Bab al-Mandeb hanya ce mai muhimmanci ga kasuwancin duniya, tana hada Tekun Ja da Gulf of Aden tare da saukaka zirga-zirgar mai da kaya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yemen - Wani babban jami’i a gwamnatin ‘yan Houthis a Yemen ya gargadi mai tsauri ga shugaban Amurka, Donald Trump.
Ya bayyana cewa za su iya rufe mashigar Bab al-Mandeb idan manufofin Donald Trump suka ci gaba.

Source: Facebook
Hussein al-Ezzi mataimakin ministan harkokin waje a Sanaa, ya bayyana cewa idan suka dauki matakin, 'dukkan mutane da aljanu ba za su iya bude mashigar ba', cewar Al Jazeera.
Ƙasar Iran ta sake rufe mashigar Hormuz
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rigingimu kan rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi wanda ya shafi tattalin arzikin duniya, cewar Middle East Eye.
Baya ta haihu game da bude mashigar Hormuz da Iran ta yi saboda yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakanin Lebanon da Isra'ila.
Rahotanni sun nuna cewa Iran ta toshe mashigar ne saboda zargin da ta yi wa shugaban Amurka, Donald Trump kan saba yarjejeniya.
Hakan na zuwa ne yayin da ake kokarin komawa teburin sulhu tsakanin kasashen Amurka da Iran a Pakistan bayan yakin kwana 40 da suka yi.

Source: Getty Images
Gargadin da Houthis ta yi ga Donald Trump
Jami'in ya bukaci Donald Trump da sauran duniya su dakatar da manufofin da ke hana zaman lafiya, tare da amincewa da hakkokin al’ummar Yemen kamar yadda ya bayyana.
Ya ce:
“Saboda haka, ya fi dacewa Donald Trump da kuma duniya da ke da hannu a ciki su gaggauta kawo ƙarshen dukkan ayyuka da manufofi da ke hana zaman lafiya, sannan su nuna girmamawar da ta dace ga haƙƙin al’ummarmu da ƙasarmu.”
Mashigar Bab al-Mandeb Strait na daya daga muhimman hanyoyin ruwa a duniya, tana hada Tekun Ja da Gulf of Aden zuwa tashar Suez Canal.
A mafi kankantarta, mashigar tana da kusan kilomita 29, inda jiragen ruwa ke bi ta hanyoyi biyu, tana taimaka wa jigilar mai da kaya zuwa Turai da Asiya.
Gargadin tawagar Iran ga Amurka a Pakistan
Mun ba ku labarin cewa shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya tuna baya kan abin da ya faru yayin tattaunawa da Iran.
Ghalibaf ya bayyana cewa shi da kansa ya gargadi tawagar Amurka gaba da gaba kan mashigar ruwa ta Hormuz wanda ke da matukar tasiri a gudanar da tattalin arzikin duniya.
Shugaban majalisar dokokin ya bayyana cewa gargadin ya tilastawa tawagar Amurka sanyawa jirgin ruwan kasar ya koma baya yayin da ake ci gaba da rikici a yankin.
Asali: Legit.ng

