Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Syria, Al Assad da Wasu Mutum 2 Hukuncin Kisa

Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Syria, Al Assad da Wasu Mutum 2 Hukuncin Kisa

  • Wata kotu ta samu tsohon shugaban Syria, Bashar al-Assad, da laifin kisan gilla, azabtarwa da kuma aikata laifuan cin zarafin bil’adama
  • Wannan na zuwa ne bayan shari'ar da ake yi da hambararren shugaban duk da cewa ya shafe shekaru da dama ya na gudun hijira bayan an kwace mulki
  • An kuma yankewa Atef Najib, tsohon jami’in tsaron siyasa a Deraa, hukuncin kisa kan rawar da ya taka wajen murkushe zanga-zangar 2011

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Syria – Wata kotun manyan laifuka da ke birnin Damascus na Syria ta yanke wa tsohon shugaban kasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa.

Ta yi hukuncin ne bayan ta same shi da laifin kisan gilla da aka shirya, azabtarwa da kuma laifukan cin zarafin bil’adama a lokacin yakin basasar kasar.

Kara karanta wannan

Bincike ya zo ƙarshe, an ji dalilin Kanal Mohammed Ma'aji na shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Kotu ta samu Assad da laifi a Syria
Hambararren shugaban Syria Bashar Al-Assad Hoto: Bashar Al-Assad
Source: Facebook

Kafar Aljazeera ta wallafa cewa kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata,11 ga watan Agusta, 2026 yayin da Assad ke zaune a kasar Rasha bayan ficewarsa daga Syria.

An yankewa Bashar Assad hukunci

A ruwayar AP News, an kuma yanke wa kaninsa, Maher al-Assad, hukuncin kisa ba tare da ya halarci zaman kotun ba. Kotun ta same shi da laifin kisan gilla da aka shirya da kuma azabtarwa.

Haka kuma, kotun ta yanke wa Atef Najib, tsohon shugaban tsaron siyasa a yankin Deraa da ke kudancin Syria, hukuncin kisa saboda aikata laifukan cin zarafin bil’adama.

Najib, wanda hukumomin Syria suka kama a watan Janairun bara, ya kasance jagoran murkushe zanga-zangar da aka gudanar a Deraa a shekarar 2011.

Wannan mataki ya taimaka wajen haddasa rikicin da daga baya ya rikide zuwa yakin basasar Syria. A yayin karanta hukuncin, Najib yana cikin keji sanye da kayan fursuna.

Kara karanta wannan

Kwanaki 10 kafin a fara kamfen, sabani ya shiga tsakanin Atiku da ADC

Kotun ta ce laifukan da ya aikata sun hada da kisa, kashe yara ‘yan kasa da shekaru 15 da gangan da kuma azabtarwa wadda ta kai ga mutuwa.

Dalilin yanke hukuncin kisa a Syria

Wannan shi ne hukunci na farko da aka yanke wa manyan jami’an gwamnatin Assad tun bayan da sabbin hukumomin rikon kwarya suka fara gurfanar da wasu daga cikin jami’an tsohuwar gwamnati.

An zargi Al-Assad da wasu jamian gwamnati da kisa
Tsohon shugaban Syria da aka yankewa hukuncin kisa, Al-Al-ssaad Hoto: Bashar Al-Assad
Source: Facebook

Alƙali Al-Aryan ya ce shaidun da aka gabatar a gaban kotu sun tabbatar da rawar da Assad ya taka a laifukan, yana mai bayyana shi da cewa ya yi amfani da hukumomin gwamnati wajen sauƙaƙa aikata laifukan.

Rahotanni sun ce hukuncin zai kawo babban sauƙi ga al’ummar Syria, tare da taimakawa wajen warkar da raunukan da yakin ya haifar.

An kwace iko da gwamnatin Syria

A baya, kun samu labarin yadda shugaban kasar Syria, Bashar al-Assad ya tsere daga babban birnin kasar, Damascus bayan shigowar dakarun ‘yan tawaye wanda ake tabbatar sun kwace iko a kasar da kuma gwamnati.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan tawaye sun kwace iko a kasar Syria bayan kifar da gwamnatin Bashar Al-Assad lamarin na iya kawo karshen yakin basasar kasar da ya shafe shekaru 13 ana yi.

A ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024 ‘yan tawaye suka ayyana nasarar kwace iko inda suke murna a birnin. Haka zalika, an ruwaito cewa dubban fursunonin siyasa sun kubuta daga gidajen yari na gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng