Wata Sabuwa: Kasar Musulunci Ta Iran Ta Jikawa Amurka Aiki ana Shirin Komawa Teburin Sulhu
- Kasar Iran ta gindaya sharadin da zai sa ta koma zagaye na biyu na tattaunawar sulhu da Amurka, wacce aka fara a birnin Islamabad
- Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh ya ce babu ranar komawa taburin sulhu da wakilan Amurka a halin yanzu
- Ya ce idan aka cimma matsaya kan tsari da ka'idojin da za a bi a zaman, Iran na iya canza shawara ta sake tura tawaga a karo na biyu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Gwamnatin Iran ta gindaya sharadin da zai sa ta koma teburin tattaunawa a zagaye na hiyu da kasar Amurka domin duba hanyoyin samar da zaman lafiya mai dorewa.
Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun nuna cewa Iran ta ki yarda ta koma wurin tattaunawa da Amurka saboda matakan da Shugaba Trump ya dauka na sa mata takunkumi a teku.

Kara karanta wannan
Lissafi ya canza, Iran ta tura sako 'mara dadi' zuwa Amurka kan batun zaman sulhu

Source: Getty Images
Iran ta gindaya sharadin komawa zaman sulhu
A wani rahoto da tashar Al-Jazeera ta wallafa yau Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026, Iran ta ce za ta iya amincewa a ci gaba da tattaunawa bisa sharadin cimma matsaya kan tsarin da za a bi.
Kasar Musuluncin ta jaddada cewa matukar ba a tsaida tsari da ka'idojin da za a bi a zaman sulhun ba, ba za ta amince ta koma wurin tattaunawa a karo na biyu ba.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wani taro da ya halarta a kasar Turkiyya.
Ko an sanya ranar sake tattaunawa?
Saeed Khatibzadeh ya nanata cewa ba za a iya sanya ranar sabon zagayen tattaunawa da Amurka ba sai an fara cimma matsaya kan tsarin da za a bi a wannan zama.
“Har sai mun amince da tsarin tattaunawa, ba za mu iya saka rana ba,” in ji Khatibzadeh.
Ya jaddada cewa duk wata yarjejeniya da Iran za ta shiga dole ne ta kare haƙƙoƙinta ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
“Iran ba za ta amince a ware ta daga dokokin duniya ba, ko kuma ta yi watsi da haƙƙoƙinta,” in ji shi.

Source: Getty Images
Bugu da kari, wata majiya daga Iran da ba a bayyana sunanta ba ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Tasnim cewa Amurka ta gabatar da wasu tsauraran buƙatu game da tattaunawar.
Majiyar ta ƙara da cewa Iran ta sanya janye irin waɗannan buƙatu a matsayin sharadi domin ci gaba da tattaunawa tsakaninta da Amurka.
Iran ta sake rufe mashigar Hormuz
A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojojin kasar Iran ta IRGC ta sanar da sake rufe mashigar ruwa ta Hourmuz saboda takunkumin da Amurka ta sanya wa tashohin ruwan kasar.
Rundunar ta gargadi cewa za ta ci gaba da dakatar da zirga-zirga ta mashigar muddin takunkumin da Amurka ta kakabawa tashoshin jiragen ruwan Ira
Hakan na zuwa ne yayin da ake kokarin komawa teburin sulhu tsakanin kasashen Amurka dLa Iran a Pakistan bayan yakin kwana 40 da suka yi.
Asali: Legit.ng
