Iran Ta Yi wa Amurka da Isra'ila Illa, Ta Tarwatsa 'Yan Leken Asirinsu

Iran Ta Yi wa Amurka da Isra'ila Illa, Ta Tarwatsa 'Yan Leken Asirinsu

  • Isra'ila da Amurka sun samu gagarumar koma baya a Iran, inda dakarun IRGC suka tarwatsa gungun masu yi wa kasashen leken asiri
  • Dakarun sun bayyana cewa sun kama masu yi wa kasashen waje leken asiri ne a wasu yankunan da suka hada da Kerman da Mazandaran
  • Hakan na zuwa ne ne yayin da ake cigaba da caccaka tsinke game da makomar mashigar Hormuz da Iran ta rufe bayan bude shi a jiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Dakarun kasar Iran sun sanar da cewa sun yi babban kamu yayin da suka yi nasarar gano wasu da ake zargi da yi wa Amurka, Isra'ila da Birtaniya leken asiri.

Hakan na zuwa ne yayin da wa'adin tsagaita wuta da aka yi tsakanin Amurka da Iran ke shirin karewa a mako mai zuwa, inda kashen ke kara shirin tunkarar juna.

Kara karanta wannan

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz bayan ta zargi Trump da karya sharadi

Mojtaba Khamenei da wani jirgin yaki
Mojtaba Khamenei a hagu da jirgin yaki a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta wallafa cewa Gwamnatin Iran ta fadi yankunan da ta kama wadanda ake zargi da zama 'yan leken asirin kasashen waje.

Kasar Iran ta yi wa Amurka/Isra'ila illa

Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta gano tare da tarwatsa wasu kungiyoyin leken asiri da ake zargin suna da alaka da Amurka, Isra’ila da Birtaniya.

Wani rahoto ya tabbatar da labarin, yana mai ambaton bangaren leken asiri na rundunar IRGC, cewa wadannan kungiyoyi na da niyyar gudanar da ayyukan leken asiri, gina hanyoyin sadarwa da kuma tayar da rikici a cikin kasar.

Wani bayani da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa rundunar ta ce an gano su ne a jihohint Azerbaijan, Kerman da Mazandaran.

An kama 'yan leken asiri a Iran

A wani bangare kuma, ma’aikatar leken asirin Iran ta ce ta kama mutane 35 da ake zargi da kasancewa cikin wata kungiyar leken asiri ta Isra'ila.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Hukumomin Iran sun bayyana cewa sun cafke wasu 'yan kungiyoyin ‘yan ta’adda da dama, ciki har da wata da ake zargin tana da alaka da Mossad, inda aka kwato abubuwan fashewa da makamai a jihohi daban-daban.

Yahoo News ta wallafa cewa ma’aikatar leken asirin ta sanar da cewa an kama:

“Wata kungiyar ‘yan ta’adda masu neman ballewa a jihohi shida, wadda ake zargin tana da alaka da Mossad da kuma wasu kungiyoyin makiya na Amurka da Isra'ila.”

Hukumomi sun ce kungiyar na da hannu a wasu hare-haren kisa da bam a cikin jihar, ciki har da kashe jami’an leken asiri da mambobin rundunar Basij.

Donald Trump da Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu da Donald Trump a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta rufe mashigar Hormuz

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojan Iran ta sanar da cewa ta sake rufe mashigar Hormuz 'yan sa'o'i bayan bude shi.

Sojojin sun zargi Shugaban Amurka, Donald Trump da karya sharadin da aka kafa kafin Iran ta amince za ta bude mashigar a ranar Juma'a.

Iran ta bude mashigar Hormuz ne bayan tabbatar da tsagaita wuta na kwana 10 tsakanin Lebanon da Isra'ila da Amurka ta ce ta jagoranta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng