Iran Ta Sake Rufe Mashigar Hormuz bayan Ta Zargi Trump da Karya Sharadi

Iran Ta Sake Rufe Mashigar Hormuz bayan Ta Zargi Trump da Karya Sharadi

  • Baya ta haihu game da bude mashigar Hormuz da Iran ta yi saboda yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi tsakanin Lebanon da Isra'ila
  • Rahotanni sun nuna cewa Iran ta toshe mashigar ne saboda zargin da ta yi wa shugaban Amurka, Donald Trump kan saba yarjejeniya
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake kokarin komawa teburin sulhu tsakanin kasashen Amurka da Iran a Pakistan bayan yakin kwana 40 da suka yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rundunar IRGC ta kasar Iran ta ce ikon mashigar Hourmuz ya “koma yadda yake a baya” saboda ci gaba da takunkumin da Amurka ke kakabawa tashoshin jiragen ruwan Tehran.

Tun bayan fara yakin Iran da Amurka a karshen watan Fabrairun 2026 dakarun Tehran suka tabbatar da toshe Hormuz, lamarin da ya jawo tashin farashin mai.

Kara karanta wannan

Ana maganar sulhu, Trump ya yi barazanar sake sakin bama bamai a Iran

Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei a hagu, wani jirgi na tafiya a hanyar Hormuz a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta wallafa cewa Iran ta bude mashigar ne bayan tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon, amma ta sake sanar da rufe shi.

Iran ta sake rufe mashigar Hormuz

Rahotanni sun nuna cewa hedikwatar hadin gwiwar sojin rundunar Iran ta IRGC ta ce Amurka na ci gaba da aikata:

“Fashin teku da satar kayayyakin ruwa da sunan takunkumi.”

Ta kara da cewa:

“Saboda haka, ikon mashigar Hourmuz ya koma yadda yake a baya, kuma wannan muhimmiyar hanyar ruwa yanzu tana karkashin tsauraran matakan kulawa da iko na rundunonin soji,”

AP ta wallafa cewa sanarwar Iran ta cigaba da cewa:

“Har sai Amurka ta dawo da cikakken ‘yancin zirga-zirga ga jiragen ruwa da ke fita daga Iran zuwa inda za su je da kuma dawowa, matsayin mashigar Hourmuz zai ci gaba da kasancewa karkashin tsauraran matakai kamar yadda yake a baya.”

Rundunar ta gargadi cewa za ta ci gaba da dakatar da zirga-zirga ta mashigar muddin takunkumin da Amurka ta kakabawa tashoshin jiragen ruwan Iran na nan.

Kara karanta wannan

Tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran ta dawo farko, an ji halin da ake ciki

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na sauraro wani jawabi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar ta zo ne washegari bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ce takunkumin Amurka “zai ci gaba da aiki gaba daya” har sai Tehran ta cimma yarjejeniya da Amurka.

Batun tattaunawa a kasar Pakistan

A gefe guda kuma, ana ci gaba da shirye-shirye a birnin Islamabad. Ana gyara wasu hanyoyi, ana kawata wurare da furanni, sannan an dakatar da zirga-zirgar jama’a.

Ana sa ran za a tura kusan jami’an tsaro 20,000 — ‘yan sanda, sojoji da jami’an tsaro na musamman — domin taron tattaunawa da ake tsammanin zai gudana tsakanin Amurka da Iran.

Haka kuma, Shugaban rundunar sojin Pakistan, Asim Munir, ya kammala ziyarar kwanaki uku a Tehran inda ya gana da shugaban Iran, ministan harkokin waje da kuma shugaban majalisar kasar..

Trump ya yi wa Iran barazana

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi magana kan karewar wa'adin tsagaita wuta da suka yi da Iran.

Kara karanta wannan

Abin mamaki: Amurka ta taimaki kasar Musulunci ta Iran, ta yi abin alheri a Hormuz

Donald Trump ya bayyana cewa shi ma bai san hakikanin abin da zai faru ba, amma ba lallai ya kara wa'adin ba idan ya kare a mako mai zuwa.

Shugaban Amurka ya yi barazanar kai hare-haren bama-bamai masu yawa a Iran idan wa'adin ya kare ba tare da cimma wata yarjejeniya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng