Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa yana sa ran cimma yarjejeniya mai kyau da kasar Iran kafin karewar wa'adin tsagaita wuta a gobe Laraba.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa kasarsa ba ta da niyyar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta kuma dakarunta sun shirya komawa fagen yaki.
Gwamnatin Birtaniya ta hana wata ‘yar Amurka da ke da ra’ayin adawa da Musulunci, Valentina Gomez, shiga kasar kafin gangamin siyasa a London watan Mayun 2026.
Kasar Qatar ta bayyana cewa ta fara tuntubar kowane bangare tsakanin Amurka da Iran domin tabbatar da cewa tattaunawar sulhu ta tafi yadda aka tsara a Islamabad.
Kasar Iran ta sanar da cewa jirgin ta dauke da man fetur ya wuce ta kusa da tekun Oman inda gwamnatin Donald Trump ta jibge sojoji domin hanata sakat.
Alakar Isra'ila da kasashen Turai na kara kamari kan kai hare-hare Lebanon, Gaza da yakin Iran. Kasashen Spain, Slovenia da Ireland sun mika bukatar hakan ga EU.
Kasar Musulunci ta Iran ta kai korafi gaban Majalisar dinkin duniya kan batun jirgin ruwan ta da kasar Amurka ta kwace, ta ce hakan ya sabawa dokar kasa da kasa.
A labarin nan, za a ji cewa wadansu mutane da ake zargi yan damfara sun fara neman jama'a su biya su kudin wuce wa ta mashigar ruwa ta Hormuz a Iran.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa aikin kwaso sinadarin Uranium da Iran ta inganta zai kasance mai matukar wahala wanda zai dauki lokaci.
Amurka
Samu kari