"Babu Lokaci," Trump Ya Sake Maganar Tashin Hankali, Ya Mika Zabin da Ya Rage ga Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yin barazanar ci gaba da kai hare-hare Iran matukar ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba
- Trump ya bayyana cew ba shi da niyya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce za ta kare a gobe Laraba, 22 ha watan Afrilun 2026
- Har yanzu dai Iran na nuna shakku kan yiwuwar komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka saboda zargin keta yarjejeniyar tsagaita wuta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba ya da niyyar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran, wadda ake sa ran za ta kare a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2026.
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka fara tunanin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka, saboda har yanzun kasashen sun gaza cimma matsaya.

Kara karanta wannan
Duk da kalaman Trump, Iran ta fito da gaskiyar abin ya kawo cikas a tattaunawa da Amurka

Source: Getty Images
Amurka ba ta shirin kara wa'adin tsagaita wuta
Trump ya bayyana cewa ba shi da niyyar tsawaita tsagaita wuta ne a wata hira da ya yi da tashar CNBC yau Talata, 21 ga watan Afrilun 2026.
Shugaban na kasar Amurka ya ce a halin yanzu babu wani lokaci da ya rage, yana mai gargadin cewa dole ne kasar Iran ta dauki mataki cikin gaggawa.
“Ba mu da lokaci mai yawa. Iran za ta iya samun kyakkyawar makoma idan ta amince da yarjejeniya,” in ji Trump.
Wane zabi Trump ya bai wa Iran?
Ya kuma kara da ikirarin cewa shugabannin kasar Musulunci ta Iran ba su da wani zabi a yanzu illa shiga tattaunawar sulhu.
Trump ya kuma bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da lokacin tsagaita wuta wajen sake sabunga makamai, kuma yanzu a shirye suke su koma kai hare-hare idan aka bukaci hakan.
“Mun tanadi makamai sosai. Muna da alburusai da duk abin da ake bukata, mun yi amfani da wannan lokaci wajen sake kimtsa kayanmu. Mun shirya tsaf, sojojin suna cikin shirin komawa yaki a kowane lokaci," in ji shi.
Dalilin da ya sa Iran ke jan kafa
A gefe guda, majiyoyi daga Iran sun nuna cewa har yanzu kasar na cikin shakku kan shiga zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka, duk da cewa ba ta rufe kofa gaba daya ba.
Rahotanni sun nuna cewa wannan shakku ba kawai saboda rashin amincewa da Amurka ba ne, har ma da zargin cewa Amurka na karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Source: Getty Images
Sai dai shugaba Trump ya ce babu lokaci mai yawa da rage wa Iran, kuma ba ta da wani zabi fage ta rungumi tattaunawa domin samar da zaman lafiya, cewar rahoton tashar Al-Jazeera.
Qatar ta yi maganar zaman sulhu
A baya, an ji cewa Qatar ta sake sa baki kan yunkurin da ake yi na sasanta Amurka da kasar Iran domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al-Ansari ya ce kasarsa ba ta son jin an fara maganar rushewar shirin sulhu, yana mai cewa suna iya bakin kokarinsu.
Ya kara da cewa kasashen yankin Gulf na ci gaba da tattaunawa kai tsaye da bangarori daban-daban a kullum, ganin cewa rikicin ya shafi yankin gaba daya.
Asali: Legit.ng
