Wata Sabuwa: Trump Ya Koma Rokon Alfarma wajen Iran bayan Ya Dade Yana Barazana
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya mika kokon bararsa ga shugabannin Iran yayin da ake shirin sake tattaunawa zagaye na biyu
- Donald Trump wanda ya sha suka mahukunta a Tehran, ya bukaci a saki wasu mata guda takwas kafin fara tattaunawar
- Shugaban na Amurka ya nuna cewa sakin matan zai zama sharar fage kan tattaunawar da ake sa ran yi a birnin Islamabad na Pakistan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya mika kokon bararsa ga shugabannin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaba Trump ya buƙaci shugabannin Iran da su saki wasu mata su takwas, yana mai cewa yin hakan zai kasance kyakkyawan abu ga tattaunawar da za a yi.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Talata, 21 ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan
Kwana 1 kafin ci gaba da yaki, Shugaban Amurka ya fadi abin da yake tsammani daga Iran
Wace bukata Trump ya nema wajen Iran?
“Zuwa ga shugabannin Iran, waɗanda ba da jimawa ba za su shiga tattaunawa da wakilai na. Zan nuna godiya ƙwarai idan aka saki waɗannan mata"
"Na tabbata cewa za su girmama matakin da kuka ɗauka na yin hakan. Don Allah kada ku cutar da su! Zai kasance kyakkyawan share fage ga tattaunawarmu!!!”
- Donald Trump
Ɗaya daga cikin matan an bayyana ta a matsayin Bita Hemmati, wata mai zanga-zanga ce da ke da alaƙa da bore na Janairun 2026 da aka yi a Tehran.
Ba a bayyana ko su wanene sauran matan ba, amma Trump ya soki gwamnatin Iran kan tsarewa da kuma kashe masu zanga-zanga.
Trump ya soki mahukunta a Tehran
Tashar CNN ta ce Donald Trump ya sake sukar Iran kan yadda gwamnatin ke muzgunawa zanga-zanga a daidai lokacin da wa'adin cimma yarjejeniya ke gabatowa.
“Ba su son ambaton hakan, masu zanga-zanga 42,000 da ba su da makami, marasa laifi, masu zanga-zangar da ba su da makami, da yawa daga cikinsu an rataye su."

Kara karanta wannan
Trump ya saki baki, ya bayyana abin da zai iya faruwa a zama na 2 tsakanin Amurka da Iran
"Don haka ba muna tattaunawa da mutane mafi kirki ba ne, amma muna tattaunawa da su cikin nasara sosai."
- Donald Trump

Source: Getty Images
Tsohon jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei ya amince cewa an kashe dubban mutanen Iran a lokacin tarzomar da aka kwashe fiye da makonni biyu ana yi a ƙasar a farkon wannan shekarar.
A wancan lokacin, Ayatollah Ali Khamenei ya ɗorawa Trump alhaki, inda ya ce ya “ƙarfafa wa masu zanga-zangar gwiwa a fili” ta hanyar yi musu alƙawarin “taimakon soja” na Amurka.
Trump ya gargaɗi shugabannin Iran cewa zai ɗauki “tsatstauran mataki” idan gwamnatin ta ci gaba da kashe masu zanga-zanga.
Shugaba Trump ya sake ba Iran zabi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya nuna cewa baya tunanin sake tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.
Shugaban na kasar Amurka ya ce babu wani lokaci da ya rage, yana mai gargadin cewa dole ne kasar Iran ta dauki mataki cikin gaggawa.
Shugaba Donald Trump ya kuma kara da ikirarin cewa shugabannin kasar Musulunci ta Iran ba su da wani zabi da ya rage musu illa shiga tattaunawar sulhu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng