"Abu 1 Muke Tsoro," Qatar Ta Tsoma Baki kan Batun Tattaunawar Sulhun Amurka da Iran
- Qatar ta sake sa baki kan yunkurin da ake yi na sasanta Amurka da kasar Iran domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya
- Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al-Ansari ya ce kasarsa ba ta son jin an fara maganar rushewar shirin sulhu
- Ya jaddada cewa Qatar da sauran kasashen yankin Gulf na ci gaba da tuntubar juna domin ganin wannan tattaunawa ta gudana yadda aka tsara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Qatar - Kasar Qatar ta bayyana cewa tana ci gaba da tuntubar dukkan bangarorin da abin ya shafa, ciki har da Amurka, dangane da shirin tattaunawar da za a yi a Islamabad.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al-Ansari, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai yau Talata, 21ga watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan
"Ta yaudare mu sau 2," Iran ta sake tona asirin Amurka ana shirin komawa teburin sulhu

Source: Getty Images
Al-Ansari ya kuma jaddada muhimmancin shiga tsakani domin cimma mafita ta siyasa da kawo karshen yakin Amurka da Iran baki daya, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta rahoto
Ya ce Qatar na ganin shiga tsakani wata hanya ce mai inganci idan har za ta taimaka wajen kusantar da bangarorin zuwa ga warware rikicin cikin lumana.
Abin da Qatar ba ta son ya faru
Al-Ansari ya ce kasarsa ba ta son a fara maganar cewa tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ta rushe, tana mai jaddada muhimmancin sulhu da zaman lafiya.
“Ba mu son a ce tattaunawar ta rushe. Duniya baki daya na goyon bayan wannan tattaunawa, ciki har da mu, kuma muna goyon bayan ‘yan uwanmu a Pakistan,” in ji shi.
Ya kara da cewa kasashen yankin Gulf na ci gaba da tattaunawa kai tsaye da bangarori daban-daban a kullum, ganin cewa rikicin ya shafi yankin gaba daya.
Rikicin Hormuz ya shafi duniya
Dangane da batun rufe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, Majed Al-Ansari ya ce warware wannan matsala ba aikin kasa daya ba ne, illa na dukkan kasashe.
Ya gargadi cewa ci gaba da rufe mashigar zai mayar da rikicin daga na yankin zuwa na duniya baki daya.
Ya kuma bayyana cewa tasirin rufe mashigar ya fara bayyana har a rayuwar yau da kullum, ciki har da batun wutar lantarki da dumamar yanayi a wasu kasashe.

Source: Getty Images
Qatar ta jaddada cewa dole ne kasashen duniya su hada kai domin kawo karshen wannan rikici, wanda zai ba da damar sake bude mashigar ruwa da dawo da zirga-zirga yadda ya kamata.
Al-Ansari ya ce Qatar za ta ci gaba da tattaunawa da abokan hulda domin nemo mafita mai dorewa, kamar yadda kafar yada labarai ta Al-Arabiyya ta ruwaito.
Iran ta garzaya Majalisar Dinkin Duniya
A baya, an ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai korafin Amurka ga Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kula da Harkokin Jiragen Ruwa.
A wata sanarwa dama'aikatar harkokin waje ta fitar, Iran ta bayyana lamarin a matsayin haramtacce kuma rashin tausayi daga bangaren Amurka.
Sanarwar ta nuna cewa matakin da Amurka ta dauka ya saba wa dokokin kasa da kasa, tare da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ake kokarin aiwatarwa a halin yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

