Sojoji Sun Daƙile Mayaƙan Wata Ƙabila da Ke Shirin Afkawa Garuruwan Fulani
- Sojojin Operation Enduring Peace sun dakile wasu mayakan Berom dauke da makamai, wadanda ake zargin sun nufi kai hari kan al’ummomin Fulani a Mangu
- Sojojin sun yi arangama da mayakan a Makera da Kaduno, lamarin da ya tilasta musu janyewa zuwa yankin Jos East bayan musayar wuta
- Rundunar ta tura karin dakaru na Special Forces domin taimakawa wajen bin mayakan da suka tsere, tare da hana sake kai hare-hare kan al’ummomin yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Mangu, Plateau - Rundunar sojojin Najeriya ta yi nasarar dakile wani yunkurin tayar da tarzoma da ya shafi fadan kabilanci a jihar Plateau.
Sojojin Operation Enduring Peace (OPEP) sun yi arangama da wasu mayakan Berom dauke da makamai, bayan samun rahoton cewa suna shirin kai hari.

Source: Facebook
Kokarin da sojoji suka yi a Plateau
Wata majiya daga rundunar sojin ta shaida wa Zagazola Makama cewa dakarun Sub-Sector 81, tare da karin sojoji, sun isa yankin da misalin karfe 7 na safe.
An tura dakarun ne a ranar 11 ga Agusta, 2026, bayan samun rahoton sirri kan motsin mayakan daga karamar hukumar Barkin Ladi zuwa Mangu.
Rahotanni sun ce mayakan na kan hanyarsu zuwa al’ummomin Gwomgada, Dorong da Kaduno, da ke gundumar Langai a karamar hukumar Mangu.
Daga bisani, sojojin sun yi wa mayakan dirar mikiya a yankunan Makera da Kaduno, inda aka yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Arangamar ta tilasta wa mayakan janyewa daga yankin, inda suka nufi babban yankin karamar hukumar Jos East, yayin da sojojin suka bi bayansu.
A halin yanzu, dakarun na ci gaba da bin sawun mayakan da suka tsere domin hana su samun damar sake kai hare-hare kan al’ummomin yankin.
A wani mataki na kara karfin rundunar, an kuma tura wasu dakaru na Special Forces daga hedkwatar Operation Enduring Peace domin taimakawa sojojin da ke gudanar da aikin.
Rundunar ta ce ana sa ran samun karin bayani kan aikin yayin da sojoji ke ci gaba da kokarin dakile barazanar da kuma kare al’ummomin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke fasto da sojoji kan shirya sace matan manyan malaman addini a Plateau
A halin yanzu, dakarun na ci gaba da bin sawun mayakan da suka tsere domin hana su samun damar sake kai hare-hare kan al’ummomin yankin.
A wani mataki na kara karfin rundunar, an kuma tura wasu dakaru na Special Forces daga hedkwatar Operation Enduring Peace domin taimakawa sojojin da ke gudanar da aikin.
Rundunar ta ce ana sa ran samun karin bayani kan aikin yayin da sojoji ke ci gaba da kokarin dakile barazanar da kuma kare al’ummomin da abin ya shafa.
Sojoji sun yi ƙoƙarin a fadan kabilanci
Kun ji cewa rundunar sojoji ta hana wata mummunar arangama tsakanin wasu mayakan Fulani da Mwaghavul a yankin Mangu na Plateau.
Sojojin sun kai ɗauki bayan samun rahoton musayar wuta tsakanin ƙungiyoyin biyu a kusa da kogin da ya raba Gaude da Aloghom.
Bayan shiga tsakani, sojoji sun mamaye yankin tare da fara matakan dawo da zaman lafiya, yayin da ake kokarin hana ramuwar gayya.
Asali: Legit.ng
