Iran Ta Nuna Jan Wuya, Jirginta Ya Tsallake Tarkon da Amurka Ta Kafa a Teku
- Kasar Iran ta sanar da cewa jirgin man ta ya koma gida ta ruwa duk da gargadi da barazanar Amurka bayan jibge sojoji a kusa da mashigar Hormuz
- Tun bayan tsagaita wuta da aka yi tsakanin Amurka da Iran shugaba Donald Trump ya ajiye sojoji da jiragen yaki domin kawo wa Iran cikas
- Matakin shugaba Trump ya sanya Iran toshe mashigar Hormuz bayan bude shi, lamarin da ya kara dagula kasuwar man fetur da gas a fadin duniya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Rundunar sojin Iran ta sanar da cewa wani jirginta ya samu nasarar wucewa ta mashigar Hormuz kusa da inda Amurka ta ajiye sojoji.
Amurka ta sanya sojoji da jiragen yakin a kusa da Tekun Oman ne domin hana jiragen ruwan Iran sakat da niyyar tilasta mata amincewa da yarjejeniya.

Source: Getty Images
Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa Gwamnatin Iran ta sanar da cewa jirginta ya wuce ta kusa da sojojin Amurka a yau Talata, 21 ga Afrilun 2026.
Jirgin Iran ya ketare barazanar Amurka
Iran ta bayyana cewa wani jirgin ɗaukar man fetur nata ya samu shiga cikin ruwan yankinta duk da gargadi da barazana da dama daga rundunar ruwan Amurka.
Yayin da take bayani kan dabarun da jirgin ya yi ya wuce, Iran ta ce:
“Duk da gargadi da barazana da dama daga rundunar ruwan Amurka, jirgin Sili City, tare da goyon bayan rundunar ruwan sojojin kasar da cikakken tsaro, ya shiga ruwan yankin Iran bayan ya tsallaka teku a daren jiya,”.
Sojojin sun kara da cewa jirgin ya kasance a daya daga cikin tashoshin jiragen ruwa na Kudancin kasar na tsawon wasu awanni yanzu.
Batun kwace jirgin Iran a teku
Wannan lamari ya zo ne bayan rundunar Amurka ta sanar a ranar Lahadi cewa sojojin ruwanta sun kwace wani jirgin ɗaukar kaya mai tutar Iran mai suna Touska a tekun Oman bayan an ce ya ki bin umarnin takunkumi.
Rahoton tashar Al Jazeera ya bayyana cewa kasar Iran ta yi Allah-wadai da wannan mataki, tana mai kiran sa da “ba bisa ka’ida ba.”
CENTCOM ta ce sojojin Amurka sun tilasta wa jiragen kasuwanci 27 su juya ko su koma wata tashar jiragen ruwa na Iran tun bayan da Amurka ta fara kakaba takunkumin ruwa a ranar 13 ga Afrilun 2026.

Source: Getty Images
Tashin hankali a yankin ya karu tun bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare tare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Ana so EU ta rabu da Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin kasar Spain ta bukaci kungiyar kasashen Tarayyar Turai (EU) ta raba hanya da kasar Isra'ila.
Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da Benjamin Netanyahu ya jagoranta a kasar Lebanon a kwanan nan da kuma luguden wuta a Gaza.
Kasashen Ireland da Slovenia sun goyi bayan Spain, inda suka bukaci kasashen Turai su sake nazari kan alaka da Isra'ila a wani zama da za su yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

