Davido Ya Ballo Aiki, Shehu Sani Ya Tanka kan Kai Batun Zaben Osun gaban Trump

Davido Ya Ballo Aiki, Shehu Sani Ya Tanka kan Kai Batun Zaben Osun gaban Trump

  • Tsohon Sanata Shehu Sani ya yi watsi da kiran Davido na neman Donald Trump da kasashen duniya su sanya ido kan zaben gwamnan Osun
  • Sanata Shehu Sani ya ce kokarin jawo Trump cikin harkokin zaben Najeriya ba zai haifar da wani amfani ba
  • Tsohon sanatan ya ce Trump na da wasu muhimman batutuwa da suka fi daukar hankalinsa a gida da wajen Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sanata kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Shehu Sani, ya yi watsi da kiran fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido.

Sanata Shehu Sani ya yi watsi da kiran na Davido na neman Shugaban Amurka Donald Trump da kasashen duniya su sanya ido kan zaben gwamnan jihar Osun mai zuwa.

Shehu Sani ya yi martani ga Davido
Sanata Shehu Sani da David Adeleke wanda aka fi sani da Davido Hoto: Shehu Sani, Davido
Source: Facebook

Da yake mayar da martani kan kiran, Sani ya ce a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X cewa hankalin Trump ya karkata ga wasu muhimman batutuwan kasa da kasa da kuma na cikin gida.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya jawo magana, ya bukaci masoyansa su kashe abokan hamayyarsa

Davido dai ya yi kira ga Trump da kasashen duniya da su sanya ido sosai kan zaben gwamnan Osun da za a gudanar ranar 15 ga Agusta, sakamakon fargabar yiwuwar tashin hankali da kuma zargin yunkurin murde sakamakon zaben.

Shehu Sani ya mayar da martani

Sanata Shehu Sani ya bayyana kokarin shigar da Trump cikin harkokin zaben Najeriya a matsayin aikin banza, yana mai cewa shugaban Amurkan bai damu ba kan sahihancin zabubbuka a kasashen Afirka.

Ya ambaci mashigar tekun Hormuz, rikicin Gaza da yakin Ukraine a matsayin wasu daga cikin batutuwan da ke bukatar kulawar shugaban Amurkan a halin yanzu.

Shehu Sani ya kuma yi nuni da zaben Majalisar Dokokin Amurka da ke tafe, inda ya ce jam'iyyar Republican ta Trump na mayar da hankali wajen ci gaba da rike tasirinta a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.

“Wadanda ke kokarin jawo Mista Trump cikin zabukanmu suna bata lokacinsu ne kawai,” in ji Sani.

Kara karanta wannan

Fitaccen mawaki ya ɗauki abubuwan da ke faruwa a Najeriya ya kai gaban shugaban Amurka

Trump ya bambanta da Obama

A cewar tsohon sanatan, Trump ya bambanta da tsofaffin shugabannin Amurka Barack Obama da Joe Biden wajen yadda yake kallon harkokin Afirka da zabubbuka.

“Trump ba Obama ba ne ko Biden. Ba shi da wata babbar sha'awa kan sahihancin zabubbuka ko akasin haka a Afirka,” in ji shi.

Shehu Sani ya kawo zabubbukan Tanzania, Uganda da Kamaru a matsayin misalan zabukan kasashen Afirka da ya ce Trump ya nuna karancin sha'awa a kansu.

“Zabubbukan Tanzania, Uganda da Kamaru misalai ne,” ya kara da cewa.

Sani ya kara jaddada cewa shugaban Amurkan na da wasu batutuwan da suka fi gaggawa, inda ya ce:

“Abubuwan da ke gaban Mista Trump sun hada da batun mashigar tekun Hormuz, Gaza da Ukraine; kuma mafi muhimmanci, jam'iyyarsa na fafutukar tsira a zabukan Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da ke tafe.”
Shehu Sani ya yi wa Davido martani
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani Hoto: Shehu Sani
Source: Facebook

An shirya gudanar da zaben gwamnan jihar Osun ranar 15 ga Agusta, yayin da jam'iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki ke kara kaimi wajen shirye-shiryen zaben.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya zargi Jingir da rura wutar rikici bayan kalamansa kan Muslim Muslim

Abin da Tinubu ya gayawa Adeleke kan zaben Osun

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayyana yadda tattaunawarsu ta kasance da Shugaba Bola Tinubu.

Gwamna Adeleke ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi masa alkawarin za a gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng